Mun kashe Qasim al-Rimi a kasar Yemen – Inji White House

Mun kashe Qasim al-Rimi a kasar Yemen – Inji White House

A Ranar Asabar da ta gabata, fadar shugaban kasar Amurka, ta tabbatar da kisan Qasim al-Rimi, wanda ta ce ta kashe ba tare da fadin inda hakan ya faru ba.

Fadar White House ta fito ta yi gajeren jawabi ta na mai cewa:

“Bisa umarnin Mai girma shugaban kasa Donald J. Trump, Amurka ta kai wani hari a cikin kasar Yemen, inda ta samu nasarar ganin bayan Qasim al-Rimi.

Wata jaridar Amurka ta bayyana cewa an kashe Al-Rimi a cikin Watan Junairu, wasu kwanaki kadan kenan kafin gwamnati ta fitar da wannan bayani.

An hallaka ‘Dan ta’addan ne a Yemen, amma babu wani karin bayani da ya fito a game da inda aka rutsa sa kamar yadda rahotanni su ka bayyana a makon jiya.

"A karkashin jagorancin Qasim al-Rimi, kungiyar Al-Qaeeda ta kai wasu munanen hare-hare marasa kyawun gani." Inji fadar shugaban kasar Amurkar.

KU KARANTA: 'Dan Sanda ya mutu a sanadiyyar arangama da 'Yan ta'adda

Mun kashe Qasim al-Rimi na kasar Yemen – Inji White House
Trump ya sa an kashe wanda aka taba tunanin zai gaji Al-Zawahiri
Asali: Twitter

Wannan ya sa Dakarun su ka kai hari domin kashe wannan gawurtaccen ‘Dan ta’adda. A ‘yan watannin nan, Amurka ta kashe manyan ‘yan ta’adda uku.

Kafin nan gwamnatin Amurka ta sa kudi har fam dala miliyan 10 ga duk wanda ya iya fada mata inda Al-Rimi ya ke a dalilin zargin ta’adin da ke kansa.

Ana zargin cewa akwai hannun wannan ‘Dan ta’adda wajen tada bam a ofishin Jakadancin kasar Amurka da ke babban birnin Yemen na Sana’a a 2008.

“Kasar Amurka, da manufar ta da abokan huldarta za su samu zaman lafiya a dalilin mutuwarsa.” Inji fadar. Al-Rimi ya taba yunkurin tada wani jirgin Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel