Jami’an hukumar kwastam sun sha ruwan duwatsu a wata babbar kasuwar Legas

Jami’an hukumar kwastam sun sha ruwan duwatsu a wata babbar kasuwar Legas

Wata kazamar rikici ta auku tsakanin jami’an hukumar yaki da fasa kauri, kwastam da yan kasuwa dake babbar kasuwar bajekoli ta ‘Trade Fair’ dake garin Ojo na jahar Legas, inji rahoton Aminiya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a sanadiyyar wannan rikici an samu jama’a da dama da suka samu munanan rauni. Rikicin ya kaure ne a daidai lokacin da jami’an kwastam tare da Sojoji suka dira kasuwar da nufin kai samame tare da kwace haramtattun kayayyaki da aka shiga dasu kasuwar.

KU KARANTA: Taskar Kannywood: Gwamnatin Ganduje ta bude ma Sani Danja kamfaninsa da ta garkame

Hukumar kwastam ta bayyana cewa ta samu bayanin sirri dake nuna akwai tarin haramtattun kaya da aka shiga dasu kasuwar daga kasar Benin ta iyakar Najeriya da kasar na kan tudu dake garin Seme.

Sai dai yan kasuwar sun ki amincewa kwastam ta shiga shagunansu domin gudanar da binciken haramtattun kayayyakin, kai da lamari yayi kamari sai yan kasuwan suka shiga jifan jami’an kwastam da duwatsu.

Da kyar shuwagabannin kasuwar suka shiga tsakanin bangarorin biyu, amma duk da haka sai da jami’an hukumar kwastam suka afka wasu manyan shaguna dake katafaren Jigawa Complex da Adamawa Plaza inda suka kwashi shinkafa da man girki.

Tun bayan garkame iyakokin Najeriya ne hukumar kwastam take bin kasuwanni da manyan rumfuna domin gudanar da bincike a kan haramtattun kayayyakin da gwamnati ta hana shigowa dasu kasa.

A wani labarin kuma, babban sakataren hukumar tace fina finai na jahar Kano, Alhjai Ismai’ila Na’Abba Afakallahu ya bayyana cewa gwamnatin jahar Kano ta bude kamfanin daukan hotuna na Sani Danja da ta garkame a kwanakin baya.

Sai dai Afakallau ya musanta rahotanni dake nuna cewa gwamnati ta garkame kamfanin ne tun da farko saboda siyasa, saboda a cewarsa sun rufe kamfanoni fiye da 20 tare da na Sani Danja sakamakon suna aiki ba bisa ka’ida ba.

Afakalallu yace Sani Danja ya kai shekaru biyu yana gudanar da kamfanin nasa ba tare da mallakar takardun da ake bukata wajen bude kamfani ba, sa’annan sun aika masa takardar gayyata domin sanar dashi matsayin da kamfaninsa yake ciki, amma ya ki amsawa, har sai da suka rufe kamfanin.

Amma Afakallahu yace sun bude kamfanin a yanzu bayan Danja ya mallaki dukkanin takardun da ake bukata. Sai dai duk kokarin da majiyarmu ta yi na jin ta bakin Sani Danja game da lamarin ya ci tura sakamakon bai amsa sakon kar ta kwana da aka tura masa ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng