Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Balarabiya ‘yar kasar Saudiyya tayi ridda ta bar addinin Musulunci

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Balarabiya ‘yar kasar Saudiyya tayi ridda ta bar addinin Musulunci

- Wata matashiyar budurwa ‘yar asalin kasar Saudi Arabia ta sha suka bayan da ta walaffa hotonta da kayan wanka tare da wani tsoho da nikab

- Rahaf Muhammad Al-Qunun ta bayyana ‘yancin da ta samu bayan ta bar ‘yan uwanta tare da barin Musulunci inda ta koma kasar Canada

- ‘Yan kasar Saudi Arabia din sun caccaketa tare da nuna kyamar abinda tayi don kuwa cewa suka yi tsiraici take son fitarwa

Wata matashiyar budurwa ‘yar asalin kasar Saudi Arabia ta sha caccaka daga jama’a bayan da ta wallafa hotonta na da sanye da niqab tare da na yanzu inda take sanye da kayan wanka a kasar Canada.

Rahaf Mohammed al-Qunun dai ta gudu ne daga kasar Saudi Arabia bayan da ta je wani hutu a kasar Kuwait. Ta kira hakan da babban kalubalen da ta taba fuskanta a rayuwarta.

Bayan wallafa hotunan nata guda biyu, Rahaf ta ce tafi son rayuwarta ta yanzu don kuwa a wancan lokacin kamar an take mata ‘yancinta ne.

Masu iya kalubale na kasar Saudi sun caccaketa ta hanyar cewa tsiraicinta take son nunawa, wanda kuwa ta san ba haka da yawan matan kasar Saudi Arabia suke ba.

Amma kuma ta samu jinjina da goyon baya daga wajen wasu mutane wadanda ke kallon guduwar da tayi a matsayin jarumta da gwarzantaka, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Tirkashi: An kai karar jaririya 'yar wata 6 kotu

Bayan wallafa hoton da tayi, wata mai bin ta a kafar sada zumuntar ta ce tana matukar jin tausayinta. Ta ce matan kasar Saudi yanzu ana barinsu su yi rayuwar farin ciki kamar kowa. Suna iya tuki, zuwa kasuwa sannan suna iya balaguro su kadai.

Matar ta ci gaba da cewa Rahaf ai da ba ta tafi ba don kuwa Annabi Muhammad ya ce mata da maza duk daya suke.

Idan bamu manta ba, a kwanakin baya ne ‘yan uwan Rahaf suka yi niyyar kasheta bayan ta gudu daga gida tare da sanar da cewa ta bar Musulunci.

Daga baya majalisar dinkin duniya ta bata kariya sannan kuma an bata masauki a kasar Canada.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Balarabiya ‘yar kasar Saudiyya tayi ridda ta bar addinin Musulunci
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Balarabiya ‘yar kasar Saudiyya tayi ridda ta bar addinin Musulunci
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel