Sarkin Rano ya nada Nura trekker a matsayin 'Sarkin Zumuncin Rano'

Sarkin Rano ya nada Nura trekker a matsayin 'Sarkin Zumuncin Rano'

A ranar Laraba ne Sarkin Rano, Alhaji Tafida Ila ya nada Nasiru Aliyu Batsari a matsayin Sarkin Zumuncin Rano.

Nasiru Aliyu Batsari dai ya yi tattaki ne a kasa tun daga Katsina har zuwa jihar Kano don nuna goyon bayansa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Idan zamu tuna, Nura Aliyu Batsari mai shekaru 33 dan asalin karamar hukumar Batsari ne da ya taka a kasa tun daga jihar Katsina zuwa Kano. Tafiya ce mai nisan kilomita 172 a titi, don nuna farin cikinsa a kan nasarar da Ganduje ya samu a kotun koli.

Sarkin Rano ya bawa Nura trekker sarauta a masarautarsa
Sarkin Rano ya bawa Nura trekker sarauta a masarautarsa
Asali: Twitter

Nura ya sanar da manema labarai cewa ya bar Katsina ne kuma Kano ya tinkara da kafa don taya Gwamna Ganduje murnar jaddada nasararsa da aka yi a kotun koli.

Ya ce, "Nayi alkawarin in har Ganduje ya yi nasara a kotun koli, zan taka a kasa daga Katsina zuwa Kano don taya shi murna. Ina yin hakan ne don nuna goyon bayana gare shi tare da jinjinawa nasarorinsa."

Sarkin Rano ya bawa Nura trekker sarauta a masarautarsa
Sarkin Rano ya bawa Nura trekker sarauta a masarautarsa
Asali: Twitter

Bayan isarsa Kano, Batsari ya samu kyakyawar tarba daga mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Nasiru Gawuna da kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Kankia/Kusada/Ingawa a tarayya, Hon. Abubakar Yahya Kusada.

Hakazalika, Gwamna Ganduje ya nuna jin dadinsa a kan kokarin Batsari na zuwa taya shi murnar nasarar a kotun koli.

A takardar da mataimakin gwamnan na musamman a fannin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fitar, ya ce: "Wannan matashin ya cancanci yabo da jinjina sakamakon nuna goyon bayansa ga jiha ta".

Ganduje ya kara da cewa, za a shirya ma matashin tarba ta musamman tare da liyafa a gidan gwamnatin jihar don karrama sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel