Da amincewar hukuma: Fasto yana sayar da wani ruwa mai a roba N13400, ya ce yana maganin 'Coronavirus'
- Angel Daniel Obinim ya ce man warakar da ya samo yana yakar cutar Coronavirus
- Faston ya kaddamar da wannan man ne a cocinsa a yayin da mambobi suka garzayo bauta
- Ana siyar da shi kan naira dubu goma sha uku ne da dari hudu kuma ana shafe jiki da shi ne a matsayin riga-kafi
Faston kasar Ghana mai abun mamaki mai suna Angel Bishop Daniel Obinim ya kaddamar da wani man waraka mai yakar cutar Coronavirus.
Shugaban cocin International God's Way din ya kaddamar da wannan man warakar ne a ranar Lahadi da ta gabata yayin da yake wa'azi a cocin.
Kamar yadda ya ce, barkewar cutar Coronavirus din a kasar China ta dame shi kuma yana tsoron cewa cutar za ta iya sauka a kasar Ghana. A don haka ne ya yanke shawarar kirkiro man warakan don yakar cutar.
Ya ce za a shafa man a duk jiki ne don bada kariya daga cutar.
Ana siyar da man ne kan N13,400 kuma sashen aljannan na FDS ta aminta da shi kamar yadda Obinim ya bayyana.
DUBA WANNAN: Abinda Abdulmumin Kofa ya fada a kan Ganduje bayan ya ziyarce shi (Hotuna)
A wani labari na daban, cutar Coronavirus na ci gaba da yaduwa kamar yadda labari daga kasar China ke bayyanawa.
A yayin da gwamnatin kasar China me kokarin samo maganin cutar, masu bincike da masana kiwon lafiya na kasar da ma nahiyar na ta samun muguwar cutar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng