Yanzu-yanzu: 'Yan fashi da makami sun kai hari a banki, an rasa rayuka

Yanzu-yanzu: 'Yan fashi da makami sun kai hari a banki, an rasa rayuka

Ana tsoron rasa rayukan mutane masu tarin yawa bayan fashi da makamin da aka yi wa wani banki a garin Ile Oluji da ke hedkwatar karamar hukumar Ile Oluji/Oke-Igbo ta jihar Ondo a ranar Alhamis.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, 'yan fashi da makamin sun hari wani babban banki ne a garin.

An yi fashin ne a ranar Alhamis da rana a karamar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo da ke jihar Ondo din. A yayin harin, an rasa rayukan a kalla mutane hudu sakamakon harbin da 'yan fashi da makamin suka dinga yi.

Hukumomin 'yan sandan jihar Ondo din sun tabbatar da aukuwar lamarin yayin da gidan talabijin din Channels suka tuntubesu.

Yanzu-yanzu: 'Yan fashi da makami sun hari wani banki
Yanzu-yanzu: 'Yan fashi da makami sun hari wani banki
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shege-Ka-Fasa: Arewa za ta kafa rundunar tsaronta na musamman (Hotuna)

Amma kuma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ondo din, Femi Joseph, ya kasa bada bayanin yadda lamarin ya faru.

Ya sanar da cewa hukumar tuni ta tura jami'an ta zuwa inda abin ya faru don fara bincike. Amma kuma har yanzu ba a tabbatar da ko su waye suka rasa rayukansu ba yayin harin.

Wani ganau ba jiyau ba ya sanar da gidan Talabijin din Channels cewa 'yan fashin sun samu shiga cikin bankin ne ta hanyar amfani da wasu abubuwa masu fashewa.

An gano cewa wasu maharba sun zamo kalubale ga 'yan fashi da makamin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel