Ban taba zargin Buhari da El-Rufai da kirkiro kungiyar Boko Haram ba – Ribadu

Ban taba zargin Buhari da El-Rufai da kirkiro kungiyar Boko Haram ba – Ribadu

Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ya bayyana cewa sharri, karya da kage ake masa da ake yayata cewa wai ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai da zargin su suka kirkiro kungiyar Boko Haram.

Ribadu ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 6 ga watan Feburairu, sanarwar da ta samu sa hannunsa da kansa, inda yayi kira ga hukumomin tsaro dasu gudanar da bincike tare da kamo wadanda suka kitsa wannan magana.

KU KARANTA: Buhari ya rantsar da wasu sabbin jiragen yaki 3 na rundunar Sojan sama

Ban taba zargin Buhari da El-Rufai da kirkiro kungiyar Boko Haram ba – Ribadu
Ban taba zargin Buhari da El-Rufai da kirkiro kungiyar Boko Haram ba – Ribadu
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa: “Da misalin wannan lokaci na shekarar da ta gabata wani sako ya yi ta yawo da ake ikirarin daga wajena ya fito, sakon yana cewa wai na fallasa yadda aka kirkiri kungiyoyin yan bindiga a sassan kasar nan.

“Da fari na yi watsi da batun saboda na dauke shi a matsayin cin fuska saboda a tunanina babu wani mai hankali da zai yarda da shi, amma sakon ya yi ta ruruwa, hakan tasa a ranar 17 ga watan Yuli na shekarar 2019 na musanta shi a shafina na Twitter.

“Amma abin haushi, bayan watanni shi da musanta sakon, mutanen da suka kirkiro sakon sun cigaba da watsa shi domin kawo matsala a cikin al’umma, don haka ina kara jaddada cewa ban taba furta wadannan kalamai ba, ban san wani abu game da abin da sakon ya kunsa ba, don haka jama’a su yi watsi da shi.” Inji shi.

Daga karshe Ribadu ya yi kira ga hukumomin tsaron da abin ya shafa dasu gudanar da bincike a kan asalin sakon tare da kamo duk masu hannu a ciki saboda a cewarsa duk masu watsa labarun karya, musamman wanda zai kawo tashin hankali a al’umma, bai kamata a kyalesu ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu sababbin jiragen yaki guda 3 mallakin rundunar Sojan sama a kokarin da gwamnatinsa ta ke yin a shawo kan matsalolin tsaro da suka yi ma Najeriya katutu.

Buhari ya kaddamar da jiragen ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Feburairu, inda ya rantsar da wasu jirage guda biyu kirar Agusta 109P helicopter da wani guda daya samfurin Mi0171E helicopter.

A jawabinsa, shugaba Buhari yace gwamnatin tarayya a karkashin shugabancinsa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta magance matsalolin tsaron da suka addabi yan Najeriya, don haka yace gwamnatinsa ba za ta baiwa yan Najeriya kunya ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel