Siyasar jihar Kano: An kama mawakin Kwankwasiyya da yayi wakar 'A wanki gara'

Siyasar jihar Kano: An kama mawakin Kwankwasiyya da yayi wakar 'A wanki gara'

- A ranar Talata 4 ga watan Fabrairu na 2020 ne wasu jami’an tsaro suka kama wani mawakin siyasa

- Matashin mawakin mai suna Muhammadu Buhari wanda aka fi sani da Kosan waka mazaunin jihar Katsina ne

- Dan Kwankwasiyya ne kuma mawaki ne ga Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari

A ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu na 2020 ne wasu jami’an tsaro na jihar Kano suka kama wani sanannen mawakin siyasa da ke jihar Katsina. Sunan mawakin Muhammadu Buhari wanda aka fi sani da ‘Kosan Waka’.

Matashin mawakin dan gaba-gaba ne kuma dan gani kashenin kungiyar Kwankwasiyayya ne. Yana daya daga cikin mawakan Gwamnan jihar Katsina, Hon. Aminu Bello Masari.

Muhammadu Buhari ko kuma Kosan waka, na wakar shi ne da salon Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara.

Siyasar jihar Kano: An kama mawakin Kwankwasiyya da yayi wakar 'A wanki gara'
Siyasar jihar Kano: An kama mawakin Kwankwasiyya da yayi wakar 'A wanki gara'
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Fim Magazine ta ruwaito, ana zargin kama Kosan waka yana da nasaba ne da wata waka da ya saki a ranar Lahadi mai suna ‘A wanki gara’.

Mujallar fim tayi kokarin gano inda aka wuce da mawakin a Kano da kuma wanda ya kai karar shi har aka kai ga damkar shi, amma hakan ba ta samu ba.

KU KARANTA: An bayyana Sheikh Ibrahim Saleh a matsayin mutum na 2 a duniya da yafi kowa ilimin Hadisi

Ba yanzu ba dai mawaka da ‘yan fim ke kokawa da yadda ake musu dauki dai-dai ana garkamesu sakamakon banbancin siyasa da ke tsakaninsu da gwamnati.

A cikin shekarar 2019 ne aka kama Naziru Ahmad, Sarkin wakan sarkin Kano. An kama mawakin ne sakamakon zargin shi da aka yi da mallakar dakin fitar da waka a cikin gidanshi.

Amma kuma ‘yan fim da dama sun danganta kamen nashi da banbancin siyasa da gwamnatin jihar Kano wacce ta sa aka hada baki da hukumar tace fina-finai don musguna mishi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel