Kotu ta bada umarnin a kashe magidanci ta hanyar rataya saboda ya kashe matarsa

Kotu ta bada umarnin a kashe magidanci ta hanyar rataya saboda ya kashe matarsa

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Jabi ta yanke hukuncin kisa a kan wani matashi dan shekara 38, Eric Chigbor, ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin kisan kai, inda ya kashe matarsa.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya,NAN, ta ruwaito rundunar Yansanda ta tuhumi Eric da aikata laifin kisan kai, inda rundunar ta ce laifin ya saba ma sashi na 220 na kundin hukunta manyan laifuka, kuma kundin ya tanadi hukunci ga duk mai laifin a sashi na 221.

KU KARANTA: Taskar Kannywood: Sani Danja ya yi korafi game da rufe kamfaninsa da gwamnatin Kano ta yi

Majiyarmu ta ruwaito a ranar 3 ga watan Feburairun 2015 ne Eric ya garzaya da gawar Jessica zuwa asibiti a garin Bwari inda ya shaida ma masu kula da gawa cewa Jessica ta kashe kanta ta hanyar kurbar fiya fiya, amma makwabtansa suka karyata shi, inda suka ce dukanta yake yi, har ya kulle kofa don kada a bata agaji.

Da yake yanke hukunci, Alkalin kotun, mai sharia Charles Agbaza ya bayyana cewa dukkanin hujjojin da ake gabatar gaban kotu sun tabbatar da cewar Eric ne ya kashe matarsa Jessica, kuma da gangan ya kashe ta ba tsautsayi ba.

Alkalin ya yi fatali da magiyar wanda ake karan na neman sassauci, inda yace duba da kwararan hujjojin da kotu ta samu game da wannan laifi, babu yadda za’a ya amince da bukatar neman sassauci da Eric ya nema daga wajensa.

“A wannan lamari, kotun ta kama wanda ake kara da laifin kashe matarsa Jessica a ranar 3 ga watan Feburairu na shekarar 2015, don haka an yanke masa hukuncin daya dace da shi. Amma kafin kotu ya furta hukuncin da ta yanke masa, ya kamata a sani, a wannan lamari, wanda ake kara ba shi da hurumin neman afuwa saboda hukuncin da doka ta tanadar.

“Don haka kamar yadda sashi na 221 na kundin hukunta manyan laifuka ta tanada, hukuncin da ya dace da shi duba da laifin daya aikata na kisa kai shi ne hukuncin kisa, hakan zai zama izina ga sauran jama’a, musamman a wannan lokaci da ake samun fadace fadace tsakanin ma’aurata.

“Kotu ba ta da hurumin zartar masa da wani horo, amma dole ne a gudanar da doka yadda ya kamata a kowanne lokaci, kuma a duk halin da aka tsinci kai. Hukuncin na nufin za’a rataye ka a wuya har sai ka mutu, da fatan Allah Ya yi maka rahama.” Inji shi.

Alkalin ya karkare hukuncinsa da sanar da wanda aka yanke ma hukuncin kisan cewa yana da daman daukaka kara idan bai gamsu da hukuncinsa ba cikin kwanaki 30.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel