Ba mu da dakin karkashin kasa: EFCC ta mayarwa Shehu Sani martani

Ba mu da dakin karkashin kasa: EFCC ta mayarwa Shehu Sani martani

Hukumar yaki ta masu yi wa arzikin kasa ta'annati EFCC ta karyata rahotannin da aka wallafa a kafafen watsa labarai na cewa tana ajiye wadanda ake zargi da aikata laifuka a dakin ajiye mutane na karkashin kasa a ofishinta.

Hukumar ta fitar da wannan sanarwar ne sakamakon jawabin da tsohon Sanata mai wakiltan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi inda ya zargi hukumar da tsare shi a dakin ajiye mutane na karkashin kasa na tsawon kwanaki 30.

Shugaban shiyya na hukumar, Mista Aminu Aliyu, yayin zantawa da manema labarai a harabar hukumar ya ce babu wani irin dakin ajiye mutane mai wannan na'uin a hukumar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ba mu da kurkukun karkashin kasa: EFCC ta mayarwa Shehu Sani martani
Ba mu da kurkukun karkashin kasa: EFCC ta mayarwa Shehu Sani martani
Asali: UGC

Aliyu ya kara da cewa ya gayyaci manema labaran domin zaga wa da su tare da wayar musu da kai kan yadda ake gudanar da ayyukan hukumar ne domin magance munanan zaton da wasu ke yi wa hukumar.

Ya ce wasu daga cikin wadanda ake zargi sun fi gwammace su dawo hukumar a ajiye su bayan an gurfanar da su a kotu a maimakon kai su gidan gyaran hali.

Ya ce: "Kamar yadda ku ka gani, ba mu da dakin ajiye mutane na karkashin kasa a nan. Mafi yawancin wadanda ake zargi su kan roki alkalai su bari a dawo da su nan saboda irin wurin ajiyar da muke da shi.

"Suna cin abinci da kowa ke ciki sau uku a nan kuma mu na da karamin asibiti da ake kulawa da wadanda suke ajiye a nan idan suna bukatar taimakon gaggawa.

"Idan wani na tunanin anyi shiri na musamman ne a yau, yana iya dawo wa a kowanne lokaci da ya ga dama domin ya gani wa idonsa.

"Idan kuna son kai ziyara duk wani ofishin mu a kasar nan, babu bukatar ma ku sanar da mu kafin ku zo. Kuna iya yin tawaga ku zo idan mutum na tsoron zuwa shi kadai."

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa an zaga da manema labaran zuwa wuraren da ake ajiye wadanda ake zargi a ginin hukumar da ke Idiagbon House, wani gini mai bene hawa hudu a Wuse II Abuja wanda shi ne hedkwatan hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel