Babu gaskiya cikin maganarka - CAN ta yiwa Buhari raddi kan wadanda Boko Haram suka fi kashewa

Babu gaskiya cikin maganarka - CAN ta yiwa Buhari raddi kan wadanda Boko Haram suka fi kashewa

Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN ta fusata da maganar shugaba Muhammadu Buhari cewa kashi 90 na wadanda Boko Haram ke kashewa Musulmai ne.

Kungiyar ta bayyana cewa wannan jawabi ya nuna karara gwamnatin Buhari na siyasantar da rayukan mutane.

Diraktan yada labaran kungiyar, Kwamkur Samuel, a hirar da yayi da Punch, yace:

"Kungiyar Kiristocin Najeriya na bayyana bacin ranta kan jawabin karya, mara asali da hujja, da shugaba Buhari yayi na cewa kashi 90 na wadanda Boko Haram ke kashewa Musulmai ne.

"Karanta irin wannan jawabin ban haushin daga shugaban kasa, ko shakka babu Buhari bai fahimci ainihin wadanda ake kashewa ba dubi ga irin hare-haren da ake kaiwa Kiristoci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel