Wata sabuwa: Kungiyar 'yan madigo sun kai karar hukumar CAC gaban kotu a Abuja

Wata sabuwa: Kungiyar 'yan madigo sun kai karar hukumar CAC gaban kotu a Abuja

- Wata kungiyar 'yan madigo ta maka hukumar kula da rijistar kamfanoni wato CAC a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja

- Kungiyar ta zargi hukumar ne da take mata hakkinta kamar yadda kundin tsarin mulki ya bata saboda kin yi mata rijista

- A shekarar 2018 ne dai babbar kotun tarayya tayi watsi da karar kungiyar bayan ta kafa hujja da sashi na 4 na dokar hana auren jinsi daya ta 2013

Wata kungiyar 'yan madigo ta maka hukumar yi wa kungiyoyi rijista a gaban kuliya. Ta zargi hukumar da kin yi mata rijistar kungiyar.

Kamar yadda sananniyar mai rajin kare hakkin dan Adam mai suna Pamela Adie, wacce ta mika karar tace, ita da kungiyarta sun yanke shawarar daukaka karar hukuncin babban kotun tarayya wacce tayi watsi da kara CAC da suka kai.

Wata sabuwa: Kungiyar 'yan madigo sun kai karar hukumar CAC gaban kotu a Abuja
Wata sabuwa: Kungiyar 'yan madigo sun kai karar hukumar CAC gaban kotu a Abuja
Asali: Facebook

Adie ta jaddada cewa rashin yi wa kungiyarta rijista ya take hakkinta da kundin tsarin mulkin kasar nan ya bata, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta ruwaito.

Kamar yadda ta wallafa a shafinta na tuwita, "kamar yadda wasu daga cikinmu suka sani, na bukaci yi wa kungiyata rijista amma sai CAC ta hana saboda kungiyar madigo ce.

KU KARANTA: Kyawun surar Ronaldo da tsawonshi ya sanya naji babu wani wanda nake so a duniya kamar shi - Georgina Rodriguez

"Hakan yayi karantsaye ga hakkina da kundin tsarin mulkin kasar nan ya bani. Ni da kungiyata mun maka CAC a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a 2018. A cikin shekarar ne kuwa aka yi watsi da karar yayin kafa hujja da sashi na 4 na dokar hana auren jinsi daya ta 2013.

"A matsayinmu na masu bin dokar kasar nan, mun daukaka kara zuwa kotun daukaka kara da ke Abuja a Najeriya.

"Ina godiya ga duk masu goyon bayanmu wajen fafutukar neman adalci a lokacin da muke bin komai ta yadda ya dace don ganin mun mori 'yancinmu da kundin tsarin mulkin kasar nan ya bamu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel