Gangar danyen man Najeriya ya koma $54 a kasuwannin Duniya

Gangar danyen man Najeriya ya koma $54 a kasuwannin Duniya

Idan mu ka koma bangaren tattalin arziki, za mu ji cewa farashin gangar danyen mai ya yi kasa sosai a kasuwannin Duniya a cikin ‘yan kwanakin nan.

Darajar mai ya sauko ne bayan da cutar Coronovirus ta barke a kasar Sin. Yanzu abin da ake saida gangan man Najeriya na Brent Crude shi ne fam Dala 54.

Gwamnatin Najeriya ta ci burin saida danyen mai a kan Dala $57 a wannan shekara ta 2020. Raguwar wannnan farashi zai girgiza tattalin arzikin kasar.

A duk rana ta Allah, Najeriya ta na sa ran saida ganguna miliyan 2.18 na danyen mai a kan akalla fam Dala $57. Yanzu kuma man ya karye zuwa Dala $54.

Burin gwamnati shi ne ta samu Naira Tiriliyan 2.64 daga mai a bana. Sauran kudin shigan da gwamnati ta ke sa ran samu daga wasu hanyoyin bai haka ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da manyan Sojojin Najeriya

Gangar danyen man Najeriya ya koma $54 a kasuwannin Duniya
A jiya da dare aka koma saida danyen mai a kan $54
Asali: Depositphotos

A duk rana Najeriya za ta rasa kusan Dala miliyan 7 daga abin da ta yi lissafi a hasashen kasafin kudi. A kudin Naira za a rasa kusan 2,350,000,000 a kullum.

A farkon watan jiya na Junairu, man Najeriya ya kai Dala 70 a kasuwa jim kadan bayan Amurka ta kashe babban Sojan kasar Iran, Janar Qassem Soleimani.

Tun daga nan kuma farashin gangar mai ya rika raguwa kasa har ya kai $54.39 a farkon makon nan. A makon jiya an saida danyen man a kasuwa a kan $60.

A yau 4 ga Watan Fubrairu da kuma Laraba ne kungiyar OPEC ta kasashen da ke fita da mai za su yi wani zama domin duba tasirin da annobar da ta shigo ta yi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel