Bayan watanni 10 a hannu, dan bautan kasa kirista ya bayyana dalilin da yasa yake son cigaba da zama tare da Boko Haram

Bayan watanni 10 a hannu, dan bautan kasa kirista ya bayyana dalilin da yasa yake son cigaba da zama tare da Boko Haram

Wani matashi kirista mai suna Abraham Amuta wanda mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta yi garkuwa dashi tsawon watanni 10 ya watsa ma masu kokarin ceto shi kasa a ido, inda ya bayyana musu ya gwammace ya cigaba da zama da yan ta’addan Boko Haram.

Daily Trust ta ruwaito Boko Haram ta kama Amuta ne a ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2019 yayin da yake aikin yi ma kasa hidima, NYSC, a jahar Borno, inda a ranar Lahadi, 2 ga watan Feburairu ya ki amincewa da tayin da Boko Haram ta masa na komawa gida.

KU KARANTA: Manoma 2 sun gamu da ajalinsu a gonakansu a hannun yan bindiga dadi

Bayan watanni 10 a hannu, dan bautan kasa kirista ya bayyana dalilin da yasa yake son cigaba da zama tare da Boko Haram
Abraham Amuta
Asali: Facebook

Bayan doguwar tattaunawa, Amuta ya bayyana ma mutanen da suka shiga har cikin dajin Sambisa da nufin amso shi daga hannun Boko Haram cewa shi fa ba zai koma gida ba, domin kuwa ya sauya addininsa, ya fita daga addinin Kiristanci.

Amuta dan asalin jahar Benuwe ya fada hannun Boko Haram ne a lokacin da suka kai wani samame a hanyar Gwoza zuwa Maiduguri yayin da suka nufi garin Chibok don kai ma jama’an garin kayan agaji. Sauran mutanen da yan ta’addan suka sata sun hada da Moses Oyeleke da Ndagliya Ibrahim Umar.

Sai dai bayan watanni bakwai a hannun yan ta’addan, Boko Haram ta saki Fasto Oyelek a watan Nuwambar shekarar 2019, kuma majiyar Legit.ng ta bayyana cewa an cigaba da tattaunawar sako sauran mutanen har sai lokacin da Amuta yace ba zai koma gida ba.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sanye da kayan Sojoji da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun bude ma wasu babbar motar Luxurious wuta a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja inda suka ji ma mutane hudu rauni.

Wannan lamari ya faru ne a gab da kauyen Gada-Biyu dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a ranar Lahadi, 2 ga watan Feburairu, inda yan bindigan suka bude ma motar kamfanin Chisco wuta mai lamba AGL 11 XL.

Direban babbar motar mai suna Madu Francis ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 5:47 na yamma a lokacin da yake gangarawa Gada-Biyu, kwatsam sai ganin wasu mutane sanye da kakin Sojojo sun fito daga cikin daji sun bude musu wuta da bindigu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel