Gwamnatin Buhari ta gurfanar da manoma dubu 70 gaban kotu saboda rashin biyan bashin N17bn
Gwmanatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta shigar da karar kimanin manoma dubu 70 a jahar Kebbi da suka gagara biyan bashin tallafin kudin noma da gwamnatin ta basu wanda ya kai naira biliyan 17.
A watan Nuwambar shekarar 2015 ne dai gwamnatin Najeriya ta kaddmar da tsarin tallafin noma ga manoman shinkafa da alkama a jahar Kebbi mai suna Anchor Borrower Scheme, inda ta basu bashin N17bn domin tallafa musu, wanda zasu biya ba tare da kudin ruwa ba.
KU KARANTA: Shuwagabannin PDP sun gudanar da zanga zanga a ofishin Amurka da Birtaniya
Daily Trust ta ruwaito shugaban kungiyar manoman shinkafa ra RIFAN reshen jahar Kebbi, Muhammad Sahabi Augie ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 2 ga watan Feburairu yayin da yake ganawa da manema labaru a Birnin Kebbi.
Augie ya bayyana cewa daga cikin manoma dubu 70 da suka ci gajiyar wannan tsari, kimanin manoma 200 ne kacal suka iya biyan kudin da suka amsa, sa’annan ya mayar da martani ga jam’iyyar adawa ta PRP da ta yi zargin ana cin zarafin manoma ne, inda yace dukkanin wadanda aka gurranar manoma ne na hakika, kuma sai da aka tantancesu kafin aka basu kudin.
Don haka Malam Augie ya kara da kira ga yan siyasa dasu kauce ma furta ire iren kalaman nan, wanda yace zasu iya hana manoman jahar cin gajiyar irin wannan tagomashi daga gwamnati a nan gaba.
“Duk hanyar da muka bi domin karbo kudaden daga manoman ya ci tura, don haka muka fara gurfanar dasu gaban kotu, a yanzu haka muna kotun majistri, kuma mun baiwa kotun jerin sunayen manoman da suke rike da kudaden.
“Yawancin manoman sun dauka sun ci banza ne, yasa har ma wata jam’iyyar siyasa ta fito tana ikirarin wai tsarin tallafin bai amfanar da jahar da komai ba, mu kuma mun san cewa kafin kaddamar da tsarin, tan dubu 70 na shinkafa ake samarwa a jahar nan, amma zuwa 2016 ya haura tan miliyan 1.2
“Wannan ya tabbatar da lallai manoman shinkafa na gaske suka samu wannan tallafi ba wai yan siyasa ba, domin kuwa da ba don haka ba da adadin shinkafar da aka noma bai karu ba.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng