Bizar Amurka: Fadar Shugaban kasa ta yi wa Atiku Abubakar gyara

Bizar Amurka: Fadar Shugaban kasa ta yi wa Atiku Abubakar gyara

Har yanzu ana ta faman ce-ce-ku-ce game da haramtawa ‘Yan Najeriya da wasu kasashen Duniya damar samun bizar zama a Amurka ta din-din-din.

Fadar shugaban kasa ta fito ta yi karin haske game da ikirarin da Atiku Abubakar ya yi na cewa Najeriya ta shiga Tawagar Operation Desert Storm a tarihi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa Najeriya ta na cikin kasashen Afrika da su ka shiga yakin Amurka domin ceto Kuwait a shekarun 1990s.

Jagoran hamayyar na Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi wannan ikirari ne a lokacin da ya fitar da wasu sakonni a kan shafinsa na Tuwita a jiya Ranar Asabar.

‘Dan takarar shugaban kasar na PDP a 2019 ya dauki lokaci ya na tofa albarkacin bakinsa game da matakin da gwamnatin Amurka, har ya ba Najeriya shawara.

KU KARANTA: Ana iya dakatar da sabon tsarin bizar shiga kasar Amurka

Jim kadan bayan Atiku Abubakar ya yi wannan magana, fadar shugaban kasa ta fito ta na mai masa raddi da cewa sam ba gaskiyar abin da ya faru ba kenan.

Gwamnatin kasar ta kuma bayyana cewa a zahiri har yanzu Najeriya ta na samun kyakkayawar alaka da Amurka, akasin abin da Atiku ya ke rayawa jama’a.

“Akwai bukatar a fayyace kuskuren da wannan sako ya ke kunshe da shi. Najeriya ba ta shiga cikin Tawagar Operation Desert Storm ba.” Inji fadar shugaban.

“Za mu kara tabbatar da cewa ainihin halin da ake ciki a kasa ya sha banban da wannan ra’ayi. Kuma Najeriya na cigaba da samun kyakkyawar alaka da Amurka.”

A tsakanin 1990 zuwa 1991 ne Amurka ta hada taron-dangi ta yaki Saddam Hussein bayan kasar Iraki ta kai wa kasar Kuwait mai arzikin man fetur farmaki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel