Ina wadanda su ka kashe Malam Albani Zariya a 2014 su ka shige?
A farkon Fubrairun 2014 wasu ‘Yan bindiga su ka kashe babban Malamin addinin nan watau Muhammad Auwal Adam wanda aka fi sani da Albani Zariya.
An hallaka Malamin ne a hanyarsa ta komawa gida a Unguwar Gaskiya bayan ya yi karatun darasin Hadasi a Makaranta kamar yadda ya saba kusan kullum.
‘Yan bindiga sun tare shi a hanya, su ka buda masa wuta a Ranar 1 ga Watan Fabrairun 2014, su ka kashe shi tare da wata daga cikin Mai dakinsa da kuma ‘Dansa.
Bayan kusan wata guda da wannan kisa, jami’an hukumar DSS su ka kama wasu mutane da ake zargin cewa su ne ke da hannu wajen hallaka Bajimin Malamin.
Kamar yadda DSS su ka bayyana a lokacin, shugaban ‘Yan Boko Haram na Yankin Kaduna da kewaye, Yakub Abdullahi ne ya kitsa yadda aka kashe Malamin.
KU KARANTA: Sun kashe Budurwa sun kona gawarta a Jihar Taraba
Sauran wadanda ke da hannu a wajen kisan Malamin sun hada da Yasir Salihu, Ibrahim Shuaibu, Bilyaminu Usman, Sahabi Ismail, Umar Ismail, da Musa Abubakar.
“Kiyayya ga Malamin ya sa ‘Yan ta’addan su ka zauna a karkashin Jagorancin Yakub Abdullahi a Unguwar Hayin Danmani a Rigasa, su ka dauki wannan mataki.”
A cewar DSS, an yi ta kai shirin ganin bayan Malamin amma sai a farkon Fubrairun 2014 ne Miyagun su ka yi nasarar kashe shi cikin dare a hanyar zuwa gida.
Tun daga lokacin da Bilyaminu Usman ya tabbatarwa Duniya cewa shi da kansa ya budawa Malamin da Iyalinsa wuta da hannunsa, ba a kuma ji wani labarinsu ba.
Shekaru shida kenan ba a ji kotu ta yankewa wadanda aka kama hukunci, ko ma an shigar da kara ba. Haka zalika ba a ji labarin inda binciken DSS din ya tsaya ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng