Babu babban bala'i a rayuwa irin mutum ya tashi ya ga an haifeshi a Najeriya - Peter Obi
- Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya bayyana cewa babban tashin hankali a rayuwa shine mutum ya tsinci kanshi a Najeriya
- Tsohon gwamnan ya bayyana hakane a lokacin da yake hira da ThisDay
- Ya ce gidansu na da matukar arziki, amma sanadiyyar yakin basasa ya sanya suka shiga kuncin rayuwa shi da mahaifiyarsa
Tsohon gwamnan jihar Anambra, kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce zama a Najeriya shine babban tashin hankalin da mutum zai tashi ya tsinci kanshi a ciki.
Obi ya bayyana hakane a lokacin da yake hira da ThisDay.
Da aka tambayeshi ko ya taba samun barazana ta rayuwa, Obi ya ce: "Akwai wata babbar barazana a rayuwa irin mutum ya tashi ya ga anyo shi a Najeriya? Kullum a cikin barazana ta rayuwa muke a Najeriya."
Da yake magana game da kasuwancin shi, Obi ya ce shi kawai ya tashi ya tsinci kanshi tsundum cikin kasuwanci ne, saboda abinda ya taso yaga iyayenshi nayi kenan.
Ya ce iyayenshi suna da arziki sosai, amma yakin basasa da aka samu a Najeriya da yayi sanadiyyar mutuwar mahaifinsa shine dalilin shigar shi matsin rayuwa lokacin yana dan shekara shida a duniya.
KU KARANTA: Yadda Jeff Bezos wanda ya fi kowa kudi a duniya ya samu dala biliyan 13 a cikin mintuna 15 kacal
"Muna da arziki sosai kafin zuwan yakin basasa, amma sanadiyyar yakin yasa muka talauce bayan mutuwar Babana lokacin ina dan shekara 6 a duniya, tun daga wannan lokacin muka shiga matsin rayuwa ni da mahaifiyata. Abu daya da wannan yakin bai dauke daga garemu ba shine gidanmu."
Da yake magana game da alakarshi da mata, Obi ya ce shi yana hada alaka da mace ne a matsayin abota ko kuma abokan aiki.
Dan takarar mataimakin shugaban kasar a babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a shekarar 2019 da ta gabata, a baya yace ya tsani kashe kudi.
Inda ya bayyana irin yadda ya gabatar da bikin aurenshi, ya ce anyi bikin gargajiya a Najeriya, sannan aka karasa bikin a coci a birnin Landan da mutane kasa da 50.
Sai dai ya ce ba kamar shi ba, "matata tana son morewa a rayuwa."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng