Kirista ya gina Masallatai guda biyu ga matafiya a garin Tafawa Balewa na jihar Bauchi

Kirista ya gina Masallatai guda biyu ga matafiya a garin Tafawa Balewa na jihar Bauchi

- Shugaban karamar hukumar Tafawa Balewa na rikon kwarya, Barista Kefas Magaji ya hada guiwa da NURTW don rage kudin mota daga Tafawa Balewa zuwa Bauchi

- Barista Kefas Magaji wanda aka fi sani da “Peace Catalyst” ya gina msallatai har biyun don direbobi da fasinjoji da ke kan hanya

- Shugaban karamar hukumar na rikon kwarya ya ce yin hakan zai wanzar da zaman lafiya tare da hadin kan addinai da kabilu a karamar hukumar

Shugaban karamar hukumar Tafawa Balewa na rikon kwarya, Barista Kefas Magaji wanda aka fi sani da “Peace catalyst” ya hada guiwa da shugabannin kungiyar ma’aikatan sufuri ta karamar hukumar wajen rage kudin mota daga Tafawa Balewa zuwa Bauchi.

Shugaban karamar hukumar na rikon kwarya ya hada kai dasu ne kuma an mayar da kudin motar N400 a maimakon N500 don tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kabilun da ka karamar hukumar. Hakan kuma zai tabbatar da yalwatar tattalin arziki a karamar hukumar.

Kirista ya gina Masallatai guda biyu ga matafiya a garin Tafawa Balewa na jihar Bauchi
Kirista ya gina Masallatai guda biyu ga matafiya a garin Tafawa Balewa na jihar Bauchi
Asali: Facebook

Barista Kefas Magaji ya kara da gina masallaci ga direbobi musulmai tare da fassinjoji. Ya kara gina wani masallaci da ke bayan rukunin shagunan Mu’azu Shuaibu don taimakwa Musulmai yin sallolinsu.

KU KARANTA: Ku yi hakuri, akwai sabon shirin da muke kokarin fito muku da shi kuma - Cewar Sadiya Umar Farouq ga ma'aikatan N-Power da za a kora

A wata takarda da mai bada shawarar shi na musamman a kan yada labarai, Folmi Barnabas Yale ya fitar, ya ce Kefas Magaji yana da burin samar da zaman lafiya tare da hadin kan addinai da jama’ar yankin.

Folmi Barnabas ya mika godiyarsu ga NURTW a kan goyon baya don ci gaban karamar hukumar da suka bada. Ya yi kira ga daukacin al’ummar karamar Hukumar Tafawa Balewa da su goyi bayan Barista Kefas wajen cimma aiyukan ci gaban da yazo wa karamar hukumar da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng