Wata sabuwa: Allah ya haramtawa mace tayi bincike a wayar mijinta - Cewar wani soja

Wata sabuwa: Allah ya haramtawa mace tayi bincike a wayar mijinta - Cewar wani soja

- Wani sojan Najeriya mai suna Bilyaminu Ladan Mada ya wallafa rubutu a kan sirrin aure a musulunci

- Bilyaminu ya ce haramun ne a musulunci mace ta taba wayar mijinta amma shi zai iya duba wayar ta saboda dukkansu mallakin shi ne

- Ya kara da cewa Ubangiji ya ba maza damar auren mata hudu, toh kuwa don miji na da budurwa ba wani abun tada hankali bane wajen matar shi

Wani sojan Najeriya mai suna Bilyamin Ladan Mada ya wallafa wani rubutu a shafin shi na Facebook mai matukar ban mamaki. Yayi magana ne a kan sirri a rayuwar auren Musulunci.

Sojan ya bayyana cewa Ubangiji ya ba maza damar auren mata har hudu idan suna da bukata.

Bilyaminu ya kara da cewa Ubangiji ya haramtawa mata bincike a wayar mazansu amma miji zai iya bincikar ta matar shi. Ya ce dalilin haka kuwa shine maza na da damar auren mace fiye da daya, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Kamar yadda ya wallafa: "Barkanmu da rana. Ina so in yi wannan bayanin a nan. Ga Musulmai, Ubangiji ya ba namiji damar auren mata hudu idan suna so kuma zasu iya adalci. Soyayya da mace kuwa ko bayan ina da aure baya nufin cin amana nake. Idan mace daya ce a gidana akwai yuwuwar in karo uku. Cin amana shi ne idan ana lalata da mata a waje.

KU KARANTA: Matashi dan shekara 18 ya yiwa Kakarsa mai shekaru 70 fyade

"Ga matan da suke ganin mijinsu na cin amanarsu idan yana soyayya da wata a waje, ga tambayata " mijinki matan shi hudu?"

"Ku sani, haramun ne mace ta duba wayar mijinta amma shi zai iya duba wayarta tare da bincike. Dalili kuwa shine "yana da damar auren mace fiye da daya. Toh idan yana da budurwa kuma matar shi ta ga hirarsu, za ta iya fusata." Gudun tashin hankali, Ubangiji ya hana dubawa miji wayar shi. Amma mijin zai iya duba wayar matar shi saboda ita da wayar mallakin shi ce kuma bata da wani sirri da za ta iya boye mishi. Don Allah ku fahimta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel