Lafiya jari: Muhimman amfanin citta 4 a jikin dan Adam
Citta na daya daga cikin sinadaren da a koda yaushe ake iya samunsu tare da sarrafa su. Hakazalika ana iya samunta a kowanne lokacin shekara. Amma kuma abun mamaki ne yadda ba mu dauke ta da wani muhimmanci ba duk da tana da matukar amfani. Citta na fatattakar mura daga jikin dan Adam.
A garinta, danya ko busasshiya, citta na da amfani kuma tana taka rawa wajen inganta lafiyar dan Adam. Ga kadan daga cikin amfanin citta kamar yadda masana kiwon lafiya suka tabbatar, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.
1. Citta na maganin tasowar amai
Tasowar amai na daga cikin alamu na zazzabi ko kuma juna biyu. Alama ce ta wasu ciwuka kuma kwata-kwata yana hana mutum sakewa. An gano cewa citta na maganin tasowar amai ko wanne iri ne kuwa.An gano cewa citta na matukar maganin tasowar amai ga masu juna biyu ballantana a laulayin watannin farko. Amma kuma akwai bukatar mace mai juna biyu ta tuntubi likita idan tana son shan citta mai yawa.
DUBA WANNAN: Maciji ya kashe wani mai wasa da macizai yayin da ya ke nuna bajintarsa (Bidiyo)
2. Citta na maganin ciwon mara yayin jinin al’ada
Ciwon mara dai na zuwa ne a kwanakin farko ko kuma kafin wasu matan su fara jinin al’ada. Wannan ciwon marar kuwa na tsananin matsantawa mata tare da hana su sakat.
A wani bincike da aka yi a kan mata 100 masu wannan ciwon marar, an bukace su da su sha citta a lokutan al'adar, kuma ya rage musu wannan ciwon ba kadan ba. Idan mace na son raguwar ciwon mara yayin jinin al’ada, sai a nemi citta a sha ta a shayi mai zafi ko kuma a tauna cittar danya.
3. Citta za ta iya hana dan Adam kamuwa da cutar kansa
Citta na da matukar amfani da masana kimiyya da fasaha ke zaton za ta iya hana dan Adam kamuwa da cutar kansa ko kuma maganinta gaba daya. Wani sinadari mai suna 6-gingerol na iya hana dan Adam kamuwa da cutar kansa. Duk da ba binciken kimiyya da fasaha ne ya tabbatar da hakan ba,, akwai yuwuwar samun maganin kansa a jikin citta.
4. Citta na yin kasa da sikarin da ke cikin jini
Ciwon siga na samun dan Adam ne bayan yawan sikarin da ke cikin jininsa ya wuce misali. Bincike ya nuna cewa citta na dauke da sinadaren da ke rage yawan sikarin cikin jinin dan Adam. Wannan binciken ya tabbatar da cewa citta na da matukar amfani ga masu cutar ciwon sikari.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng