Dalilin da yasa na ke son a samu karuwar rikici a APC - Oshiomhole
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Adams Oshiomhole, ya ce yana so a ci gaba da rikici a jam'iyyar in har hakan zai sa su zamo masu nasara.
Oshiomhole ya yi wannan jawabin ne yayin karbar masaukin 'yan jam'iyyar ta APC reshen jihar Kano, wadanda suka samu jagorancin Gwamna Umar Ganduje a Abuja.
Kamar yadda yace, rikicin jam'iyyar bai hana ta nasara ba a zabukan da aka yi cikin kwanakin nan. Oshiomhole ya ce ba zai ki a ci gaba da rikici a jam'iyyar ba matukar za ta ci gaba da samun nasarori a zabukan nan gaba, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Maciji ya kashe wani mai wasa da macizai yayin da ya ke nuna bajintarsa (Bidiyo)
"Idan na daga mujallu kuma na ga cewa ana rikici a APC amma ina juya wani shafi na ga nasarorin da aka samu a zabuka, na kan sakankance cewa rikicin ne ke tabbatar da nasarorinmu a zabuka. Kila zamu ci gaba da zama cikin rikici," ya ce.
Idan zamu tuna, jam'iyyar APC na fuskantar rikicin cikin gida, lamarin da ya jawo Gwamna Obaseki na jihar Edo ke barazanar korar Oshiomhole daga jam'iyyar a jihar.
Bayan wannan rikicin, tsohon ministan yada labarai, Tony Momoh ya jaddada cewa babu abinda ya shafi Oshiomhole da shiga sabgar jam'iyyar a jihar Edo saboda Obaseki ne shugabanta na jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng