Ganduje ne ya taimaka mini na lashe zabe - Dan Kwankwasiyya da ya kada Jibrin Kofa

Ganduje ne ya taimaka mini na lashe zabe - Dan Kwankwasiyya da ya kada Jibrin Kofa

- A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka gabatar da zaben maye gurbi na dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji

- A zaben dai tsohon dan majalisar Abdulmumin Jibrin Kofa ya sha kasa a hannun Aliyu Datti Yako

- Yako dai dan babbar jam'iyyar adawa ne na PDP, amma wata jita-jitar ta bayyana cewa jam'iyyar APC ta taimaka masa ya lashe kujerar

Zababben dan majalisar wakilai na jihar Kano mai wakiltar Kiru da Bebeji, Aliyu Datti Yako, ya bayyana irin goyon bayan da ya samu daga wajen gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wanda yasa ya samu nasara akan abokin karawarshi, Abdulmumin Jibrin Kofa.

Yako wanda ya fito takarar a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya yiwa gwamnan godiya a lokacin taron murnar samun nasararsa da aka yi a Kano.

Ganduje ne ya taimaka mini na lashe zabe - Dan Kwankwasiyya da ya kada Jibrin Kofa
Ganduje ne ya taimaka mini na lashe zabe - Dan Kwankwasiyya da ya kada Jibrin Kofa
Asali: Facebook

Gwamna Ganduje da ABdulmumin Jibrin Kofa dai duka ‘yan babbar jam’iyyar APC mai mulki ne a jihar.

Yako ya ce: “Mun dogara ga Allah akan komai, kuma ya bamu nasara. Mun tashi a mazabarmu mun ga kowa ya zama dan jam’iyyar PDP. Saboda haka ya zama tilas mu yi godiya ga shugabannin Kiru da Bebeji.

“Muna kuma mika godiya ga gwamna Ganduje, jam’iyyar APC, hukumar ‘yan sanda, hukumar INEC da sauransu da suka tsaya wajen ganin an gabatar da zabe lafiya ba tare da rikici ba.”

KU KARANTA: Najeriya ta zama 29 a duniya sannan ta 3 a Afrika cikin kasashen da suka fi iya turanci

Haka shi ma shugaban jam’iyyar PDP na jihar mai rikon kwarya, Dankaka Hussaini Bebeji, ya shiga cikin tawagar taya dan majalisar murna, haka shima ya mika godiyarshi ga gwamna Ganduje, inda yace dan majalisar zai kasance na mutum biyu ne, Kwankwaso da Ganduje.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka gabatar da zaben na maye gurbi, inda Yako ya samu nasara akan Jibrin Kofa.

Ana ta yada jita-jitar cewa akwai wata kullalliya da jam’iyyar APC ke kulawa domin ta kayar da Jibrin, sannan kuma ta nemi hanyar da Yako zai dawo jam’iyyar APC bayan ya lashe zabe.

Haka kuma an ruwaito cewa sauran ‘yan takara na sauran jam’iyyu kamar irinsu PRP, APGA, sun ajiye burinsu na fitowa takarar suka goyawa Yako baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel