Yanzu-yanzu: An sace Maigari da 'dansa a jihar Zamfara

Yanzu-yanzu: An sace Maigari da 'dansa a jihar Zamfara

Yan bindiga sun yi awon gaba da Maigarin Gayari, na karamar hukumar Gummi a jihar Zamfara, Alhaji Hassan Mouhammad, da yaronsa. Punch ta ruwaito.

Wani mazaunin garin, Malam Abubakar Sani, ya bayyanawa majiyarmu cewa yan bindigan sun dira garin Gayari ne daren Alhamis kuma suka tafi gidan gidan Maigarin sukayi gaba da shi.

A cewarsa, yan bindigan rike da bindigogi AK47 sun yi harbe-harbe domin tsorata makwabtan da suka fito.

Abubakar ya kara da cewa yaran Maigarin biyu yan bindgian suka sace amma daya ya fado daga kan babur ya dawo gida.

Yace: "Basu kashe kowa ba, sun fada masa cewa sun zo daukeshi ne. Sun hada da dansa kuma sun bayyanawa dukkan garin cewa sun hada milyan arba'in ko a kawo musu mumunan hari."

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Mohammed Saidu, ya tabbatar da labarin kuma yace suna gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel