Gwamnatin jahar Kaduna ta yi nadin sabon shugaba a hukumar jin dadin alhazai

Gwamnatin jahar Kaduna ta yi nadin sabon shugaba a hukumar jin dadin alhazai

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya sanar da sunan Malam Sani Dalhatu a matsayin sabon shugaban hukumar kulawa da jin dadin alhazai ta jahar Kaduna.

Daily Trust ta ruwaito kafin nadinsa, Malam Musa shi ne shugaban sashin ayyuka na hukumar jin dadin alhazai na jahar Kaduna, kuma ya dauki tsawon shekaru 20 yana aiki a hukumar alhazai.

KU KARANTA: Za’a samu tsaro idan muka kawar da bambancin dake tsakaninmu – Buhari ga yan Najeriya

Haka zalika Malam Musa ya taba zama shugaban kula da jin dadin alhazai a karamar hukumar Birnin Gwari, Igabi da wasu kananan hukumomi, kuma ya taba mai kula da shiyya domin jin dadin alhazai.

A wani labari kuma, Ke duniya, ina za ki damu ne? rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Taraba ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 31 wanda take zarginsa da kashe wata budurwa, tare da kona gawarta a jahar.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito saurayin mai suna Munda Bala, wanda dan asalin karamar hukumar Donga ne ya kashe budurwarsa mai suna Imabujir Ambisi ne tare da taimakon wasu miyagun abokan sa biyu.

Da yake zantawa da manema labaru, mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Taraba, David Misal, ya bayyana cewa bayan miyagun sun kashe ta, sai suka banka ma gawarta wuta, sa’annan suka binne sauran barbashinta a wani daji.

Wisal yace har yanzu suna cigaba da kokarin ganin sun kamo sauran miyagun abokan biyu da suka tsere, yayin da suke shirin gurfanar da Munda gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala gudanar da bincike a kansa.

Shi ma a nasa jawabin ga manema labaru, Munda, wanda ya bayyana sauran barbashin kasusuwa da tokan gawar budurwarsa ya tabbatar da aikata laifin, sai dai ya danganta hakan da matsin tattalin arziki da kuma bakin kishi da yake da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng