Saurayi da abokansa 2 sun kashe budurwarsa, sun kona gawarta a Taraba

Saurayi da abokansa 2 sun kashe budurwarsa, sun kona gawarta a Taraba

Ke duniya, ina za ki damu ne? rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Taraba ta samu nasarar cafke wani matashi dan shekara 31 wanda take zarginsa da kashe wata budurwa, tare da kona gawarta a jahar.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito saurayin mai suna Munda Bala, wanda dan asalin karamar hukumar Donga ne ya kashe budurwarsa mai suna Imabujir Ambisi ne tare da taimakon wasu miyagun abokan sa biyu.

KU KARANTA: Karya ta kare: Maigida ya kama matarsa a kwance da kwarto a kan gadonsa

Saurayi da abokansa 2 sun kashe budurwarsa, sun kona gawarta a Taraba
Munda
Asali: Facebook

Da yake zantawa da manema labaru, mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Taraba, David Misal, ya bayyana cewa bayan miyagun sun kashe ta, sai suka banka ma gawarta wuta, sa’annan suka binne sauran barbashinta a wani daji.

Wisal yace har yanzu suna cigaba da kokarin ganin sun kamo sauran miyagun abokan biyu da suka tsere, yayin da suke shirin gurfanar da Munda gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala gudanar da bincike a kansa.

Shi ma a nasa jawabin ga manema labaru, Munda, wanda ya bayyana sauran barbashin kasusuwa da tokan gawar budurwarsa ya tabbatar da aikata laifin, sai dai ya danganta hakan da matsin tattalin arziki da kuma bakin kishi da yake da shi.

“Soyayya ya hada ni da Imbajuri Ambisi har ta zama budurwata, sa’annan na mata ciki, kuma ta haifan min yaro namiji, amma bayan wata bakwai sai ta kashe yaron. Hakan ya matukar bata min rai, amma ban fada ma kowa ba.

“Daga nan kuma sai talauci ya fada min, yan kudadena suka kare, shi ne sai ta koma wajen wasu yara masu kudi dake cinikayya da turawa, wannan ya sa min kishi a raina sosai, shi ne na nemi shawarar abokaina, wanda suka fada min idan har ina so na samu kwanciyar hankali sai na kasheta, ka ji dalilin kashe ta.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamna Abubakar Sani Bello.

Sai dai ya gargadi yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel