Gwamnan Adamawa ya sallami ma’aikata 5,000 kan rashin bin ka’idar daukar aiki

Gwamnan Adamawa ya sallami ma’aikata 5,000 kan rashin bin ka’idar daukar aiki

- Gwamnatin jihar Adamawa ta amince da sallamar ma’aikata 5,000 da gwamnatin baya ta All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Jibril Bindow ta dauka aiki

- An tsayar da albashin ma’aikatan gwamnatin a shekarar da ya gabata akan rashin bin ka’idar daukar aiki da sauya wajen aiki.

- Kwamishinan labarai na jihar Mista Pella ya shawarci wadanda aka dauka aiki tsakanin Satumban 2018 da Mayun 2019 da su nemi sabon aiki, cewa gwamnatin ba za ta dunga daukarsu a matsayin ma’aikata ba

Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya amince da sallamar ma’aikata 5,000 da gwamnatin baya ta All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin Jibril Bindow ta dauka aiki.

An tsayar da albashin ma’aikatan gwamnatin a shekarar da ya gabata akan abunda gwamnatin jihar ta kira da “rashin bin ka’idar daukar aiki da sauya wajen aiki.”

A karshe an sallami ma’aikatan yayinda bangaren zartarwa ta jihar ta amince da rahoton wani kwamitin da gwamnatin ta nemi ya lura da daukar aiki da sauya wajen aiki a jihar.

A ranar Laraba, kwamishinan labarai da tsare-tsare, Umar Pella ya sanar da sallamar nasu bayan wata ganawa da yan majalisar zartarwa a gidan gwamnati da ke Yola.

Mista Pella ya shawarci wadanda aka dauka aiki tsakanin Satumban 2018 da Mayun 2019 da su nemi sabon aiki, cewa gwamnatin ba za ta dunga daukarsu a matsayin ma’aikata ba.

KU KARANTA KUMA: Tsaro: Abinda Buhari ya fada wa shugabannin rundunonin tsaro na kasa yayin ganawarsu

Pella ya ce rahoton kwamitin ya nuna cewa akwai rashin bin ka’ida a tsarin daukarsu aiki.

A wani labari na daban, mun ji cewa Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ne mutum daya tilo da zai iya kawo karshen yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya da suka addabi al'umma.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya bayyana hakan ne a jawabin da ya saki ranar Laraba, 29 ga Junairu, 2020.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel