Rukunin karshe na daliban Kwankwasiyya sun tashi zuwa kasashen waje biyu
A ranar Laraba ne gidauniyar Kwankwasiyya ta jihar kano ta dau nauyin dalibai tara don tafiya kasar Sudan da Daular Larabawa don yin digirinsu na biyu.
Jaridar Daily Nigerian ta ruiwaito cewa bakwai daga cikin daliban zasu yi karatun a fannin ilimin addinin Musulunci ne da harshen larabci a kasar Sudan inda sauran biyun zasu karanci fannin kasuwanci ne a Dubai.
A yayin jawabi ga daliban jim kadan kafin tashinsu, tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana cewa sune kaso na karshe na dalibai 370 da gidauniyarsa ta dauki nauyin karatunsu zuwa kasar Indiya da wasu kasashen duniyar nan.
Kwankwaso ya ce yau ta kasance rana mai dumbin tarihi don ya cika alkawarin da ya dauka na daukar nauyin ci gaban karatun matasa a ciki da wajen Najeriya.
“Wannan rana ce mai dumbin tarihi wacce muka cika alkawarinmu na ci gaba da daukar nauyin mata da matasa don ci gaba da karatunsu,” ya jaddada.
Sanata Kwankwaso, wanda ya wakilci jihar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai ta 8 ya yi kira ga daliban da su dau karatunsu da matukar muhimmanci tare da kasancewa jakadai na gari ga jiharsu da kasarse a yayin da suka sauka a Sudan da Dubai.
Kamar yadda ya ce, gidauniyar ta biya musu kudin makaranta, wajen kwana, abinci da kuma kudin kashewa.
DUBA WANNAN: Kano: Dan takarar PDP da ya kayar da Abdulmumi Kofa yana shirin koma wa APC
Abba Kabir Yusuf, dan takarar gwamnan jihar a zaben 2019 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya bukaci daliban da su kasance jakadun Kwankwasiyya nagari, jihar Kano da kuma Najeriya. Ya ce duk wanda yayi kuskure ba zai tafi haka ba, watau ba tare da an hukunta shi ba.
Ya ce gidauniyar za ta ci gaba da bin kwakwafin karatun nasu a makarantun da suka tafi.
Babban malami a jaihar, Sheikh Ibrahim Daurawa, ya ja kunnen daliban a kan nuna wata dabi'a da kan iya bata sunan jihar Kano da Najeriya a kasar da suke je da kuma idon duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng