Gwamnatin tarayya za ta a gina tituna da kudaden Abacha

Gwamnatin tarayya za ta a gina tituna da kudaden Abacha

- Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na kwato wasu karin dala miliyan 321 na tsohon shugaban kasa a mulki soja, Sani Abacha daga waje

- Ministan shari'a ya ce gwamnatin na dab da rattaba hannu tsakaninta da tsibirin jersy inda aka taskace kudin da kuma Amurka kan yadda za a dawo wa Najeriya da kudaden nan ba da jimawa ba

- Malami ya ce za a yi amfani da kudaden wajen aiwatar da aikin gina manyan tituna da suka hada da ta Lagos-Ibadan, Abuja-Kano da kuma gadar Second Niger

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na kwato wasu karin dala miliyan 321 na iyalan tsohon shugaban kasa a mulki soja, Sani Abacha daga kasashen waje.

Abubakar Malami, ministan shari’a kuma Atoni Janar na ya ce gwamnati za ta yi amfani da kudaden Abachan da za a karbo wajen aiwatar da aikin gina manyan tituna kasar.

Titunan da za a gina sun hada da ta Lagos-Ibadan, Abuja-Kano da kuma gadar Second Niger.

Malami ya ce gwamnatin na dab da rattaba hannu tsakaninta da tsibirin jersy inda aka taskace kudin da kuma Amurka kan yadda za a dawo wa Najeriya da kudaden nan ba da jimawa ba.

Gwamnatin tarayya za ta a gina tituna da kudaden Abacha
Gwamnatin tarayya za ta a gina tituna da kudaden Abacha
Asali: UGC

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwar kasar, Malami ya ce gwamnati na tattaunawa da kasashe domin kwato karin wasu kadarorin da wasu tsoffin jami'an gwamantin kasar ake zargi da sata suka taskace a kasashen ketare.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kotu ta baiwa tsohon Antoni Janar, Mohammed Adoke, belin N50m

Wadanda za a kwace kadarorin daga hannunsu sun hada da tsohuwar ministar albarkatun mai Deizani Alison Madueke da tsoshon gwamnan jihar Delta James Ibori da Kola Aluko ake zargi da satar kudaden gwamnati, daga kasashen ketare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel