An damke shugaban Miyetti Allah, yan Fulani a jihar Plateau, an garzaya dasu Abuja

An damke shugaban Miyetti Allah, yan Fulani a jihar Plateau, an garzaya dasu Abuja

- Rikicin jihar Filato na kara rinchabewa yayin da wasu mazauna garin suka kai harin ramuwar gayya a wasu unguwannin Fulani

- Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya umurci kwamishanan yan sanda ya kama dukkan Fulanin garin

- An yi asarar rayuka akalla 40 a wannan hare-haren da ake kaiwa tsakanin Fulani da yan gari

A ranar Laraba, jami'an hukumar yan sandan jihar Plateau sun yi awon gaba da shugabannin kabilar Fulani a karamar hukumar Mangu, Bokkos, Barkin Ladi da Riyom.

A yau Alhamis, 30 ga Junairu, 2020 an garzaya da su Abuja domin yi musu tambayoyi kan rikicin ya afku a Bokkos farkon makon nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa an damkesu ne bayan gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, ya umurci kwamishanan yan sandan jihar, Isaac Akinmoyede, ya damke dukkan Ardon garin da yan Fulani suka kai farmaki inda suka hallaka akalla mutane 23.

Misalin karfe 4 na asuba, an tafi da dukkan Ardon da aka damke tare da shugaban kungiyar Miyetti Allah MACBAN hedkwatan hukumar yan sanda dake Abuja.

KU KARANTA: Ado Doguwa ya gabatar da matansa 4 gaban yan majalisa, ya ce yara 27 suka haifa masa

Mun kawo muku rahoton cewa wasu fusatattun matasa a Filato sun kai hari a wasu unguwannin Fulani a jihar inda suka banka wa gidaje 23 wuta har da wani masallaci.

Ana yi wa harin kallon ramuwar gayya sakamakon kisar gilla da aka yi wa wasu 'yan jihar 13 da ake zargin makiyaya dauke da bindigu ne suka aikata a kauyen Kwatas da ke karamar hukumar Bokkos na jihar ta Filato.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel