Wani matashi na shirin fara tattaki daga Katsina zuwa Kano a gobe Juma’a don taya Ganduje murna

Wani matashi na shirin fara tattaki daga Katsina zuwa Kano a gobe Juma’a don taya Ganduje murna

Masu iya magana kan ce soyayya gamuwar jini ce kuma kowa da irin sana’ ar da ta karbe shi. Hakan ce ta kasance ga wani matashi mai suna Nura Aliyu Batsari wanda ke shirin yin tattaki daga Katsina zuwa jahar Kano.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa matsahin zai yi tattakin ne domin taya gwamnan jaha Kanor, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, murnar samun nasarar shari’ar zabe a Kotun Koli da a kammala kwanan nan.

An tattaro cewa matashi wanda ya kasance dan asalin jihar Katsina, ya sha alwashin yin wannan tattaki daga Birnin Dikko zuwa Birnin Dabo, taya Gwamna Ganduje murna, musamman saboda yadda ya ga wasu sun kafa wa gwamnan Kanon kahon zuka, amma kuma kullum Allah ya na ba shi nasara a kansu.

Wani matashi na shirin fara tattaki daga Katsina zuwa Kano a gobe Juma’a don taya Ganduje murna
Wani matashi na shirin fara tattaki daga Katsina zuwa Kano a gobe Juma’a don taya Ganduje murna
Asali: Twitter

Yin tattaki don nuna goyon baya ko nuna kauna kauna ba sabon abu bane a Najeriya. Ko a shekarun baya an samu wani masoyin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tattaki zuwa birnin Abuja daga Lagas, don taya shi murnar lashe zaben 2015.

A gobe Juma’a, 31 ga watan Janairu ne dai matashin zai fara tattakin nasa.

KU KARANTA KUMA: Hajji: Zan zabtare kudin mahajatta – Zababben Shugaban NAHCON ya yi alkawari

Ya ce: “Zan yi tattaki ne daga jahar Katsina zuwa jahar Kano in sha Allah, don taya mai girma gwamnan jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje murnar nasarar shari’a da ya yi a babbar kotun kolin Nijeriya ta ba shi, na tabbatar da shi a matsayin halastacce kuma zababben Gwamnan Jahar Kano a karo na biyu. Zan fara tattakin ne ranar Juma’a idan Allah ya kai mu.

“Na zabi Kano ne, saboda yanayin siyasar jihar da yadda a ke matsa wa gwamnan jihar, amma kullum ya ke yin nasara kan ’yan adawarsa, sannan kuma muhimmin abu shi ne irin ayyukan da mai girma gwamnan jahar Kano ya ke yi na raya kasa kama daga yadda ya ke mayar da Kano kullum kwanan duniyar nan sabon birni da kuma tsarin da ya kawo na ilimi kyauta kuma dole wannan ci gaba ne musamman ga ‘ya’yan masu masu rangwamen karfi, sannan ga shirinsa na karkara Assalamu alaikum wanda shiri ne da ake zuwa kauyuka ake jin kokensu kuma a magance mu su shi nan take. Sannan ga samar da ayyukan yi ga matasa wanda kowa ya ga yadda gwamnatin take iyakar kokarinta.

“Wannan ta sa na ga ya cancanci in yi tattaki na je na taya shi murna kuma in taya al’ummar Kano murna da samun gwamna jarumi wanda kullum yake kallon matsalar al’umma tamkar tashi. Sannan idan na je zan yi kira ga sauran ‘yan siyasa da su yi koyo da Gwamna Ganduje na jahar Kano na ayyukan alheri. Malamai su tallafa masa da addu’ar nasara sannan masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni da su tallafa masa, don ingantuwar mulkinsa.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel