Hukumar EFCC ta gurfanar da Ishiekwene, wasu 2 a gaban kotu

Hukumar EFCC ta gurfanar da Ishiekwene, wasu 2 a gaban kotu

EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta gurfanar da Mista Azubuike Ishiekwene a gaban Alkali a Ranar Laraba.

Rahotanni sun ce ana zargin Azubuike Ishiekwene da laifin da su ka shafi buga takardun bogi da nufin damfarar kudin da sun kai Naira miliyan 350.

EFCC ta shigar da karar tsohon Darektan na gidan jaridar Punch gaban Alkalin wani kotu na laifuffuka na musamman da ke Garin Ikeja a jihar Legas.

Ishiekwene ya yi tarayya da wasu wanda su ka hada da Olalekun Abdul, Adeyinka Adewale, Morakinyo Bolanle a zargin aikata wadannan laifuffuka.

Wadanda ake tuhuman duk sun hallara a gaban kotu face Adeyinka Adewale wanda bai samu zuwa ba. EFCC ta jefe su da zargin aikata tarin laifuffuka 15.

KU KARANTA: Ban damfari Mai kamfanin ASD ba - Shehu Sani

Lauyan hukumar EFCC, Joy Amahian, ya fadawa kotu cewa wadanda ake tuhuma sun yi amfani da wasu takardun kamfanin karya wajen bude asusu a banki.

Daga nan ne wadannan mutane da ke gaban kotu a yanzu su ka yi yunkurin amfani da wannan akawun wajen karbar bashin kudin banki da takardun karya.

Buga takardun bogi domin damfara ya sabawa sashe na 441, 365, 336 da kuma 335 na kundin tsarin dikokin jihar Legas kamar yadda EFCC ta bayyana.

Wadanda ake zargi sun bayyanawa kotu cewa ba su aikata laifin da ake jefe su da shi ba. Lauyan A. Adewale ya fadawa kotu cewa wanda ake nema ba ya kasar.

EFCC ta bukaci a cigaba da tsare wadanda ake tuhuma, amma Lauyansu ya ce gidajen yari sun cika. Alkali Mojisola Dada ya dakatar da shari’ar zuwa Juma’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel