Kare da akuya sun shiga takarar neman sarauta a birnin Fair Heaven na kasar Amurka

Kare da akuya sun shiga takarar neman sarauta a birnin Fair Heaven na kasar Amurka

- Wata akuya mai suna Lincoln da wani kare mai suna Sammy sun shiga gasar neman sarauta a birnin Vermont da ke Amurka

- An gano cewa manyan garin sun kirkiro wannan gasar ne don samun kudin da zasu gyarawa yaran garin wajen wasa

- Ga duk mai jefa kuri'a a zaben, zai biya dala daya wanda a zaben 2019 garin ya samu $200 a wannan dabarar

Wata akuya mai suna Lincoln da wani kare mai suna Sammy sun shiga jerin masu neman mukamin 'mayor of Fair Haven' a wani gari mai sun Vermont a US.

Manajan garin mai suna Joe Gunter ne ya sanar da manema labarai a kan yadda suka kirkiro zaben dabbobin don samun kudin da zasu gyara wajen wasan yaran garin, kamar yadda jaridar Linda Ikeji ta ruwaito.

Kare da akuya sun shiga takarar neman sarauta a birnin Fair Heaven na kasar Amurka
Kare da akuya sun shiga takarar neman sarauta a birnin Fair Heaven na kasar Amurka
Asali: Facebook

Gunter ya ce; "A Fair Haven, masu zabe basu fitowa kamar yadda ya kamata."

Karen wanda aka gano cewa na wani makiyayi ne dan asalin kasar Jamus kuma yana ziyartar makarantun garin tare da wani jami'in, yana ziyartar wajen wasa kuma ana son shi a garin, an zabe shi ne don mukamin shugaban 'yan sanda.

KU KARANTA: Matasa su fara neman ilimin aure kafin su fara yin shi - Gwamnatin jihar Kano

Ita kuwa akuyar wacce ta lashe zabe a 2019 ta shiga wannan zaben ne kuma ana zaton za ta yi nasara don ganin yadda tayi suna a garin.

Sharai Thayer mai yara uku a makarantar garin ya ce: "Muna fatan Sammy ya lashe gasar. Karen na zama a makarantar a lokutan da yaran ke shige da fice. Wani lokacin kuwa har azuzuwansu yake shiga."

Masu zabe zasu biya dala daddaya a ranar zaben da za a yi ranar 3 ga watan Maris.

Garin na bukatar $80,000 na gyaran wajen wasan amma an samu $200 daga zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel