Matasa su fara neman ilimin aure kafin su fara yin shi - Gwamnatin jihar Kano

Matasa su fara neman ilimin aure kafin su fara yin shi - Gwamnatin jihar Kano

- Daraktar kula da al’amuran mata a ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Kano, ta yi kira ga mata da maza da su nemi ilimin zamantakewa kafin fada wa aure

- Ta ce maza da mata su nemi wayar da kai a kan yadda zasu zauna da juna bayan aure don hakan zai rage sabanin da ake fuskanta

- Darakatar ta bayyana cewa a shirye suke tsaf don wayar da kan wasu daga cikin matasa maza da mata masu shirin yin aure

Daraktar kula da al’amuran mata a ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar kano, Hajiya Kubra Ibrahim Dankani ta yi kira ga matasa da ke shirin yin aure da su kasance masu ilimin aure kafin yin shi.

Hajiya Kubra Ibrahim ta bayyana hakan ne a ranar Talata a gidan rediyon Dala yayin da aka yi hira da ita.

Matasa su fara neman ilimin aure kafin su fara yin shi - Gwamnatin jihar Kano
Matasa su fara neman ilimin aure kafin su fara yin shi - Gwamnatin jihar Kano
Asali: Facebook

Ta ce: “Maza da mata su nemi ilimin zamantakewar aure kafin su yi aure saboda gudun sabani da ake samu tsakanin ma’aurata. Matsalar ita ce suna yin aure kai tsaye ne ba tare da sun san muhimmancin shi ba. Kuma mun shirya tsaf a yanzu don wayar da kan wasu daga cikin matasa maza da mata masu shirin yin aure domin basu horarwa a kan auratayya”. Cewar Kubra.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Mazaje na takura matayensu shayar da su nono a kasar Uganda

“Hakazalika, hukumar mu tana tallafawa marayu da marasa galihu a birni da karkara ta hanyar koya musu sana’o’in dogaro da kai. Duk wani mai bukatar hakan kofarmu a bude ta ke”. In ji Kubra.

Idan ba ku manta ba dai Hajiya Kubra Ibrahim ta sanar da gidan rediyon Freedom cewa gwamnatin jihar Kano za ta kawo karshen barace-barace da mata a jihar ke yi.Ta ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen tabbatar da walwalar jama’arta.

Gwamnan jihar dai ya bayyana kudurinshi na mayar da hankali wajen habaka fannin ilimi da lafiya a jihar, inda ya ce sune muhimman bangarori da za a bai wa muhimmanci idan har ana son samun cigaba a waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel