Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da tsohuwa yar shekara 82
Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai farmaki unguwar Okeriota dake yankin Ode Aye na karamar hukumar Okitipupa na jahar Ondo, inda suka yi awon gaba da wata tsohuwa mai shekaru 82 a duniya, Allice Fadeni.
Jaridar The Nation ta ruwaito tsohuwa Allice ita ce mahaifiyar wani hamshakin dan kasuwa mazaunin jahar Legas, Sehinde Fadeni, wanda aka ce an sace ta ne da yammacin Talata aka yi awon gaba da ita zuwa wani wuri da ba’a sani ba.
KU KARANTA: Rai ba a bakin komi ba: Yan fashi da makami sun bindige matashi dan bautan kasa
Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun shuga har cikin gidan tsohuwa Allice ne, inda suka daukota daga cikin dakinta, kuma har zuwa lokacin tattara rahoton nan basu tuntubi kowa daga cikin iyalanta ba.
Kaakakin rundunar Yansandan jahar Ondo, CSP Femi Joseph ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace tuni sun kaddamar da bincike a kan lamarin, kuma suna bin sawun masu garkuwan da nufin ceto matar tare da kamasu.
A wani labari kuma, gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana wasu manyan kalubale dake kawo tarnaki, tare da mayar da hannun agogo baya a yakin da Najeriya take yi da kungiyar ta’addanci na Boko Haram fiye da shekaru 10.
Zulum ya bayyana haka a ranar Talata, 28 ga watan Janairu yayin da yake gabatar da kasida a taron kara ma juna sani da kwalejin tsaro ta kasa ta shirya ma dalibanta na kwas 28 a babban birnin tarayya Abuja.
Zulum ya bayyana manyan matsaloli hudu da suka zamto kalubale ga yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas da suka hada da; cin hanci da rashawa, tserewar yan gudun hijira daga gidajensu, rashin aminci tsakanin Sojoji da jama’a da kuma rashin kyakkyawan tsari.
“Kana bukatar abubuwan da suka dace domin kawo karshen yaki, makaman da suka kamata da sauran kayan aiki, amma a yanzu wani babban matsala shi ne rashin aminci tsakanin Sojoji da jama’an gari, wannan babban matsala ne dake damunmu, akwai bukatar shawo kansa.
“Idan har jama’a basu koma garuruwansu ba, yakin ba zai kare ba, saboda akwai bukatar jama’a su koma gidajensu domin cigaba da al’amuransu na yau da kullum.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng