Kiristoci 70 sun samu tallafin karatu daga kungiyar addinin Musulunci a Nassarawa

Kiristoci 70 sun samu tallafin karatu daga kungiyar addinin Musulunci a Nassarawa

Wata kungiyar addinin Musulunci dake jahar Nassarawa mai suna Islamic Society if Eggonland, ISE, ta bayar da tallafin karatu ga akalla dalibai kiristoci 70 dake karatu a cibiyoyin ilimi daban daban a fadin Najeriya.

Daily Nigerian ta ruwaito babban sakataren kungiyar ISE, Abdullahi Galle ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin kungiyar dake karamar hukumar Nassarawa Eggon na jahar.

KU KARANTA: Maganganu 4 masu muhimmanci da Sarki Sunusi ya fada ma Gwamna Ganduje

A jawabinsa, Malam Abdullahi yace dalibai 275 ne suka samu tallafin karatun a zangon karatu na shekarar 2019/2020, kuma daga cikinsu akwai kiristoci 88 da suka nemi tallafin, amma guda 70 ne suka yi nasarar samu.

Yayin da musulmai 307 suka nemi tallafin, amma 205 ne suka samu, kamar yadda Abdullahi ya bayyana. Sakataren ya cigaba da cewa: “Manufarmu na bayar da tallafin karatun ga mabiya addinai daban daban shi ne don kara danzon zumunci da hadin kai da kuma fahimtar juna a tsakani.

“Mu kungiya ne na taimako, kuma babu addinin daya koyar da nuna wariya da bambanci, don haka muke fatan ganin jama’anmu sun hada kai sun zauna lafiya da juna. Muna da dalibai 404 tun daga shekarar 2014 da muka fara.

“Daga cikinsu akwai 188 dake karatun digiri a jami’o’i, dalibai 38 a kwalejojin kiwon lafiya da koyon jinya sai kuma 111 a kwalejojin ilimi, haka zalika akwai dalibai 5 dake digiri na uku, masu digiri na biyu guda 13 sai kuma masu babbar difloma ta HND su 20.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamna Abubakar Sani Bello.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel