An kama faston da ya kitsa garkuwa da kansa domin samun kudin fansa

An kama faston da ya kitsa garkuwa da kansa domin samun kudin fansa

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta damke wani fasto a jihar mai suna Clement James a kan garkuwa da yayi da kansa a jihar. Faston da abokin laifinsa, George Otokpa sun shiga hannu ne bayan da suka bukaci kudin fansa har Naira miliyan 5 daga hannun iyalansu.

A takardar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo yasa hannu kuma ya mika a ranar Laraba, ya ce runduna ta musamman ta cibiyar yaki da garkuwa da mutane ta jihar ce ta cafke wadanda ake zargin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar ya ce sun samu kama mutane biyun ne bayan da iyalan.su suka kai rahoton garkuwa da su da aka yi.

An kama faston da ya kitsa garkuwa da kansa domin samun kudin fansa
An kama faston da ya kitsa garkuwa da kansa domin samun kudin fansa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan majalisa sun bawa hammata iska a kan rabon fatanya

"Wanda ake zargin mai suna Clement James ya shiga hannu ne bayan da aka bibiye shi ta lambar wayarsa har aka yi sa'a aka kama shi inda ya boye kanshi yana kuma ikirarin garkuwa da shi aka yi. An kama shi ne tare da abokinsa mai suna George Otokpa mai shekaru 22 wanda da shi ne iyalanshi suke cinikin kudin fansa." in ji shi.

Ya kara da cewa, "A halin yanzu dai wadanda ake zargin suna amsa tambayoyi kuma za a gurfanar dasu a gaban kotu bayan kammala bincike,"

Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Umar M. Muri ya kushe wannan laifin kuma ya yi kira ga jama'a da su guji irin wannan rashin tausayin da kauyancin.

Kwamishinan 'yan sandan ya ci gaba da tabbatar wa da jama'ar jihar Kaduna cewa za a yi amfani da duk shaidun da aka samu a kan wadanda ake zargin ta yadda hakan zai zama jan kunne ga duk masu tunanin aikata hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel