An kama tsohon kwamishinan kuɗi a Kwara

An kama tsohon kwamishinan kuɗi a Kwara

Wata babban kotun tarayya da ke zama a jihar Kwara ta bukaci a tsare mata tsohon kwamishinan kudi na jihar, Ademola Banu, a hannun hukumar yaki da rashawa ta EFCC a kan zargin wawurar wasu makuden kudi.

An gurfanar da tsohon kwamishinan kudin tare da wasu mutane a kan zarginsu da ake da laifuka tara a gaban Mai shari'a Babagana Ashigar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

EFCC din ta zargi masu kare kansu din da laifin hada kai wajen wawurar naira miliyan dari hudu da sha daya wacce mallakin gwamnatin jihar Kwara ce.

Daya daga cikin laifukan shine: "Olarewaju Adeniyi, Ademola Banu da kamfanin Travel Messenger a tsakanin watan Janairu zuwa Disamba na 2018 sun hada kai wajen waskar da naira miliyan dari hudu da sha daya wanda mallakin gwamnatin jihar Kwara ne. Hakan ya ci karo da sashi na 18 na dokokin hana almundahanar kudade na 2012, kuma abin hukuntawa karkashin sashi na 15, sakin layi na 3 da na 4."

DUBA WANNAN: Dokar zabe: PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC

Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake zargin su a gaban kotun.

Lauyan EFCC, Nnaemeka Omewa ya sanar da babban alkalin cewa "Ya mai shari'a, bayan musanta aikata laifukan da ake zargin su da su, masu gabatar da kara suna bukatar wannan kotu mai albarka da ta saka rana don kawo shaidu. Muna kuma bukatar kotu ta bamu damar adana su a wajen gyaran hali na hukumarmu kafin a fara sauraron shari'ar."

Lauyoyin wadanda ake kara, Gboyega Oyewole da Bamidele Ibironke sun roki alkalin da ya bada belin wadanda suke karewa kuma zargin da ake musu za a iya bada beli.

Bayan sauraron kowanne bangare, Mai shari'a Ashigar ya dage sauraron bukatar belin zuwa ranar 11 ga watan Fabrairu 2020, kuma ya bada damar ci gaba da tsare wadanda ake zargin a hannun EFCC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel