Wutar lantarki: Rashin isasshen gas ya jawowa Najeriya asara

Wutar lantarki: Rashin isasshen gas ya jawowa Najeriya asara

A Ranar Litinin dinnan, masu harkar wutar lantarki a Najeriya su ka rasa fiye da Biliyan guda a sakamakon rashin isasshen gas da za ayi aiki da shi.

Naira biliyan 1.707 kasar ta yi asara a sanadiyyar matsalar gas kamar yadda gwamnatin Najeriya ta bayyana a Ranar Talata, 28 ga Watan Junairu, 2020.

Ofishin da ke ba mataimakin shugaban kasa shawara game da harkar wutar lantarki ne ya fitar da wannan jawabi a jiya kamar yadda mu ka samu labari.

Rahoton da aka fitar ya nuna cewa rashin gas ya hana kamfanonin da ke samar da lantarki su iya yin aiki a dalilin wannan matsala da ta auku a makon nan.

Kamfanonin GenCos su kan yi aiki ne da ruwa da karfin gas wajen samar da wuta. Rashin gas din shi ya jawo aka gaza samun 3, 205 megawatts na wuta.

KU KARANTA: Abin da ya sa VAT ba zai taba Talakawa ba - Ahmad Lawan

Wutar lantarki: Rashin isasshen gas ya jawowa Najeriya asara
Matsalar gas ta haifar da rashin wuta da asara a Najeriya
Asali: UGC

Haka zalika jawabin da aka fitar ya bayyana cewa a wannan rana da gas ya yi gardama, an yi asarar kusan megawatts na 150 na abin da ake samu daga ruwa.

Bayan haka, ba a iya samar da megawatt 200.1 na wutar lantarki a farkon makon nan ba saboda rashin wasu kayan da ake amfani da su wajen jan wutan.

A Ranar wannan Litinin da ta gabata, akasarin abin da kamfanonin GenCos su ka iya samarwa shi ne 3,942 a kowace sa’a kamar yadda jawabin ya bayyana.

Mataimakin shugaban kasa ya na cikin masu ruwa da tsaki wajen harkar wutar lantarki a Najeriya. Har yanzu dai sha’anin wutan ya nema ya ci tura a kasar.

Idan ba ku manta ba kwanan nan gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta batar da biliyan 1.7 a kan wuta cikin shekaru uku.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel