Yanzu-yanzu: Kayi murabus tunda ka gaza samar da tsaro - Shugaban yan PDP a majalisa ga Buhari

Yanzu-yanzu: Kayi murabus tunda ka gaza samar da tsaro - Shugaban yan PDP a majalisa ga Buhari

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Eyinnaya Abaribe, ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus kan gazawar gwamnatinsa wajen magance matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya.

Abaribe ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a zauren majalisa yayinda ake tafka muhawara kan rashin tsaro a kasar.

Yace: "Mun yan Najeriya ba IGO muka zaba ba, ba hafsoshin Soji muka zaba ba. Gwamnatin APC muka zaba a 2015. Muna kira ga wannan gwamnatin tayi murabus saboda ta gaza wanzar da hakkinta."

KU KARANTA: An kulle shagon yan kasar China a Abuja kan ha'inci da tsoron Coronavirus

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamna Abubakar Sani Bello.

Buhari yace: “Na yi mamaki matuka game da abubuwan dake faruwa a yankin Arewa maso yamma, a lokacin da muke yaki da ta’addanci mun san akwai Boko Haram, amma abin dake faruwa a yanzu abin mamaki ne. wannan abu ya fi karfin addini ko kabilanci, manakisa ce kawai ake shirya ma Najeriya.

“Daga yanzu ya zama dole mu kara zafi a kansu, daga cikin aikin dake wuyar gwamnati akwai samar da tsaro, idan bamu samar da tsoro a kasar ba babu yadda zamu tafiyar da tattalin arzikin kasar”

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Femi Adesina a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, inda ya kara da cewa samun arzikin danyen mai a yankunan Benue, Bida, Bauchi da Gombe zai kara karfin tattalin arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel