Gwamnatin Kano zata dauki mataki a kan mata masu bara

Gwamnatin Kano zata dauki mataki a kan mata masu bara

- Gwamnatin jihar Kano ta kirkiro sabbin tsare-tsare da zasu hana mata bara a titunan jihar

- Daraktar kula da harkokin mata ta ma’aikatar mata ta jihar Kano, Hajiya Kubra Dankani ce ta sanar da hakan

- Ta ce ma’aikatar mata ta bangaren ofishinta na bai wa mata masu karamin karfi tallafi don fara sana’o’in dogaro da kai

Gwamnatin jihar Kano ta kirkiro sabbin tsare-tsare da zasu hana mata bara a titunan jihar.

Daraktar kula da harkokin mata ta ma’aikatar mata ta jihar Kano, Hajiya Kubra Dankani ce ta sanar da hakan a lokacin da ta ke tattaunawa da filin Barka da Hantsi na gidan rediyon Freedom da ke Kano.

Hajiya Kubra ta bayyana cewa barace-barace da mata ke yi a titunan jihar Kano abu ne mara kyan gani wanda ta alakanta hakan da sakacin maza.

DUBA WANNAN: Bakin kishi: Wata mata ta kone kanta kurmus a jihar Kano

Ta ce duk da wannan halin da matan suka shiga a jihar Kano, ma’aikatar kula da walwalar matan jihar ta fito da tsare-tsaren da suke taimakawa mata a fadin jihar Kano din.

Ta ce ma’aikatar mata ta bangaren ofishinta na bai wa mata masu karamin karfi tallafi don fara sana’o’in dogaro da kai da sauransu.

Hajiya Kubra ta kara da cewa, baya da tallafin da suke bai wa mata, ta ce matan da suka rasa mazansu ana basu tallafi na musamman tare da biya musu kudin haya.

Hajiya Kubra Dankani ta ce gwamnatin jihar Kano ta damu matuka a game da barace-barace da mata ke yi a kan titunan jihar musamman da dare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel