Tun aka dawo demokradiyya ba'a zabe a Akwa Ibom, rubuta sakamako kawai akeyi - INEC REC

Tun aka dawo demokradiyya ba'a zabe a Akwa Ibom, rubuta sakamako kawai akeyi - INEC REC

Shugaban hukumar gudanar da zaben kasa INEC na jihar Akwa Ibom ya fasa kwan yadda magabatansa suka bar yan siyasa na cin karnukansu ba babbaka a jihar tun bayan dawowa demokradiyya.

Mike Igini ya bayyana cewa tun fil azal ba'a gudanar da zabe a fadin jihar, kawai rubuta sakamako akeyi, a baiwa wanda akeso.

Ya ce yanada hujjoji kan jawabinsa musamman a zaben shugaban kasa na 2015 da 2019.

Yace: "A shekarar 2015 a Akwa Ibom, sun baiwa shugaban kasa mai ci a yanzu kashi 5 cikin 100 na kuri'u."

Yayinda yan jarida ke kokarin jawo hankalinsa kan illar maganar, ya jaddada cewa " Lallai haka sukayi, saboda a Akwa Ibom ba'a zabe, sakamako suke rubutawa."

"Ina da hujjojin; saboda lokacin da aka tura ni Akwa Ibom; Sarakunan gargajiya, malaman addini da kungiyoyi suka kawo min ziyara, amma hakan ba sabon abu bane gareni."

Ya yi alkawarin cewa zai kawo karshen wannan abu a jihar Akwa Ibom kuma za'a ga canji.

KU KARANTA: Zazzabin Lassa: Mutane 41 sun hallaka, 258 sun kamu - Gwamnatin tarayya

Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya, ta ce ta ruguza sababbin zabukan da ta shirya a wasu bangarorin kasar nan a cikin karshen makon da ya gabata.

INEC ta bayyana cewa ta kashe zabukan da aka yi a wasu rumfunan zabe a zabukan karashen da aka shirya a Garuruwan da ke Kuros Riba da kuma Akwa Ibom.

A wani jawabi da hukumar ta aikawa Manema labarai a Ranar Talata, 28 ga Watan Junairu, aka bayyana wannan mataki da aka dauka kwanaki da yin zaben.

Kwamishinan wayar da kan jama’a da yada labarai na hukumar INEC, Festus Okoye, shi ne ya sa hannu a wannan jawabi da aka aikawa ‘Yan jarida a fadin kasar.

Okoye ya bayyana cewa hukumar INEC ta cin ma wannan matsaya ne a sakamakon sabawa dokokin zabe da aka rika yi a wadannan wurare da abin ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel