Yansanda sun tarwatsa masu garkuwa a Katsina, sun kama miyagu 5

Yansanda sun tarwatsa masu garkuwa a Katsina, sun kama miyagu 5

Rundunar Yansandan jahar Katsina ta sanar da kama wasu gungun miyagu yan bindiga guda biyar da suka shahara wajen satar mutane tare da garkuwa dasu domin neman kudin fansa a yankin karamar hukumar Safana.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansanda reshen jahar Katsina, SP Gambo Isah ne ya bayyana haka a ranar Talata, 28 ga watan Janairu yayin da yake ganawa da manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bayyana bakin cikinsa game da hauhawan matsalar tsaro a Najeriya

“A ranar Litinin, da misalin karfe 4 na rana muka tarwatsa miyagun bayan samun bayanan sirri game da ayyukansu, inda Yansanda da tubabbun yan bindiga suka kai musu farmaki har mabuyarsu.” Inji shi Gambo Isah.

Kaakakin yace a yayin da Yansanda suka fara bincikensu, miyagun sun tabbatar da satar wani karamin yaro Abdulrahman Samaila daga kauyen Runka na karamar hukumar Safana tare da garkuwa da shi inda suka nemi kudin fansa naira miliyan 3.

Haka zalika rundunar ta sanar da kama wasu hamshakan dillalan miyagun kwayoyi guda hudu a kananan hukumomin Kankia da Charanchi dake sayar da tabar wiwi da sauran haramtattun kwayoyi.

A wani labarin kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwarsa game da hauhawa tare da karuwar matsalolin tsaro a duk fadin kasar nan, duk kuwa da irin matakan da gwamnatinsa take dauka.

Buhari ya bayyana haka ne yayin daya karbi bakuncin manyan iyayen kasa da suka fito daga jahar Neja wadanda suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a karkashin jagorancin gwamnan jahar, Gwamba Abubakar Sani Bello.

Sai dai an ruwaito shi yana gargadi ga yan bindigan da suka sanya yan Najeriya cikin halin bakin ciki da damuwa, inda yace su jira matakin da gwamnatinsa za ta dauka a kansu, kuma sai sun yi kuka da kansu.

Haka zalika, Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB na nan da ransa, kuma cikin koshin lafiya kamar yadda wasu manyan hadimansa, kuma na hannun damansa suka tabbatar.

Hadiman nasa sun bayyana haka ne biyo bayan jita jitan da ake yadawa a kafafen sadarwar zamani na cewa wai IBB ya rasu da sanyin safiyar litinin, 27 ga watan Janairu. Amma majiyar ta tabbatar da cewa Babangida na cikin koshin lafiya.

Daga cikin hadiman Babangida akwai wanda yace: “A yanzu da nake magana ina gidan Baba, yana sanye da malum malum babbar riga, kuma yana cin abinci ne.”

Shi ma wani hadimin nasa yace: “Mutuwa baa bin boyewa bane, idan Babangida ya mutu a yau, ba zai taba zama jita jita ba, ba’a iya boye mutuwa saboda abu ne wanda ke kan kowa, kuma idan ya faru dole kowa ya sani.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel