Zazzabin Lassa: Mutane 41 sun hallaka, 258 sun kamu - Gwamnatin tarayya

Zazzabin Lassa: Mutane 41 sun hallaka, 258 sun kamu - Gwamnatin tarayya

Akalla mutane 41 sun rasa rayukansu a sassan Najeriya daga farkon shekarar 2020 kawo yanzu, gwamnatin tarayya ta tabbatar.

Ministan Ilimi, Osagie Ehanire, ya bayyana hakan ne ranar Talata yayinda yake hira da manema labarai a sakatariyar ma'aikatar dake Abuja.

Yayinda yake bayani kan yaduwar zazzabin, ya bayyana cewa akwai likitoci da ma'aikatan kiwon lafiya cikin matattun 41 kuma akalla mutane 258 sun kamu da cutar a jihohin Najeriya 19.

Ya yi kira ga yan Najeriya gaba daya su kasance masu tsafta da kare kayan masarufinsu daga kashi da fitsarin beraye.

Ga jerin jihohin da aka tabbatar da bullar zazzabin Lassa kawo yanzu: Abia, Bauchi, Borno, Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Kaduna, Kano, Kogi, Ogun Ondo, Plateau, Rivers da Taraba

Hakazalika, Ministan ya yi tsokaci kan bullar cutar coronavirus da ta samo asali daga kasar China, da kuma aka samu a akalla kasashen Afrika biyu.

Ya bayyana cewa ma'aikatar ta sanar da yan Najeriya akwai yiwuwar cutar ta shigo Najeriya amma har yanzu dai babu rahoton kamuwa.

Yace bullar coronavirus a kasar Ivory Coast da Kenya abin damuwa ne ga Najeriya saboda cutar nada saukin kamuwa daga mutane.

Zazzabin Lassa: Mutane 41 sun hallaka, 258 sun kamu - Gwamnatin tarayya
Zazzabin Lassa: Mutane 41 sun hallaka, 258 sun kamu - Gwamnatin tarayya
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa Akalla mutane 56 sun mutu kawo yanzu a sakamakon cutar coronavirus da ta barke a kasar Sin. Wannan cuta ta fito ne a Yankin Wuhan, kafin cutar ta fara zagaya Duniya.

Kawo yanzu akwai mutane 2000 da su ka kamu da wannan cuta a fadin Duniya. Ga jerin kasashe 12 da cutar ta bulla yanzu:

1. Kasar Sin (Daga nan aka gano ta)

2. Australiya

3. Spain

4. Japan

5. Malaysiya

6. Nepal

7. Singapore

8. Faransa

9. Taiwan

10. Koriya ta kudu (South Korea)

11. Amurka

12. Vietnam

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel