Idan kida ya canza: Baturen Italiya ya auri Mutumiyar Najeriya a Legas

Idan kida ya canza: Baturen Italiya ya auri Mutumiyar Najeriya a Legas

Wani bikin aure da aka yi tsakanin Mutumin kasar Italiya da ‘Yar Najeriya ya dauki hankalin jama’a a cikin ‘yan kwanakin bayan nan.

Labarin wannan aure ya karada wurare musamman a dandali da shafukan sada zumunta na zamani wanda Matasa su ka saba da shi.

Jama’a da-dama su na ta magana a game da wadannan hotuna da aka wallafasu a zauren Instagram yayin da ake ta gwangwajewa.

Wannan aure ya hada mutanen Kudancin Najeriya na dangin Amarya da kuma Turawan kasar Italiya da su ka fito daga bangaren Ango.

Angon ya tsalleke teku ne daga Yammacin Duniya ya fado Garin Legas domin ya auri Sahibarsa. Sunan wannan Baturen Ango Gian Carlo.

Rahotanni sun bayyana cewa an ga Angon dauke da irin kayan da Yarbawa su ke sanyawa a biki. Hakazalika ‘Yanuwansa sun yi masa kara.

Su ma ‘Yanuwa da Abokan Ango sun zuba kayan Yarbawan ne yayin da Amarya da iyayenta su ka yi ango da wasu kaya masu daukar idanu.

KU KARANTA: Kai jama'a: Ta kashe Mahaifiyarta saboda ta samu Mahaifinta

Amaryar ta sha kwalisa a bikin inda ta rika canza kaya domin burgewa. Da farko ta sa koren kaya, sai kuma ta koma ta canza ta sa jan riga.

Shi ma Angon ba a bar sa a baya ba, jama’a sun gan shi sanye da tsanwar malum-malum (babbar riga) irin ta yarbawa kafin ya buga wata farar riga.

An ga kawayen Amaryar sun sanya kaya na burgewa domin taya daya daga cikinsu murnar wannan rana ta musamman na auren ta da jar fara.

A hotunan da aka dauka, an ga tsofaffi musamman Iyayen Amaryar su na kokarin barkewa da kuka saboda tsanin farin cikin auren ‘Diyarsu.

A cikin ‘yan kwanakin nan ana samun labarin soyayyan Maza da matan kasar waje. Wannan karo Matar Najeriyar nan ce ta auri Bature.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel