Buhari ya yi sabbi nade-nade a CBN, NCC da NCAA
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi nade-nade masu muhimmanci a babban bankin kasa (CBN), hukumar harkokin sadarwa (NCC) da wata hukumar harkokin jiragen same (NCAA).
Shugaba Buhari ya amince da nada Kingsley Obiora a matsayin mataimakin babban gwamnan kasa (CBN) da kuma nada Kaftin Musa Shuaibu Nuru a matsayin babban darektan hukumar NCAA.
Kazalika, ya amince da nada darekta da kuma mamba na hukumar NCC.
A ranar Litinin ne shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya karanta takardar amince wa da nadin mutanen da shugaba Buhari ya aika wa majalisar.
DUBA WANNAN: Bauchi: Saurayi mai kishi ya caka wa budurwarsa wuka saboda ta amsa kiran wani a gabansa
A ranar 20 ga watan Janairu ne Sanata Tolu Odebiyi ya bukaci majalisar dattijai ta sahale wa shugaba Buhari ya nada mutanen bayan an karanta wasikar da ya aiko wa majalisar ta neman izininta kafin ya tabbatar da nadinsu.
Sanata Olu ya samu goyon bayan Sanata Ezenwa Oyewuchi, lamarin daya nuna cewa majalisar ta amince da bukatar shugaba Buhari ta son nada mutanen.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng