Zaben maye gurbi: 'Yan sanda sun kama mutane 3 da laifin siyan kuri'a a Kano
Rundunar 'yan sandan jihar kano ta ce ta cafke wasu mutane uku da atke zargi da siyen kuri'a da kudi a yayin zaben maye gurbi a jihar na ranar 25 Janairu.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da akamen a takardar da ya fitar a ranar talata a jihar Kano.
An yi zaben maye gurbin majalisar wakilan tarayya da na majalisar jihar ne a kananan hukumomi tara na jihar.
Kujerun majalisun tarayyar da zaben maye gurbin ya shafa sun hada da Kiru/Bebeji, Tudun Wada. Doguwa da Kumbotso. Na majalisun jiha sun hada da Madobi, Minjibir, Rogo da Bunkure.
An yi zaben cikin zamn lafiya da lumana a yankunan da zaben ya shafa.
DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota
Haruna ya ce akwai wasu matakai da rundunar ta bi kafin ta cafke wadanda ake zargin. An akam su ne da katikan zabe da kuma kudade wadanda ake zargin na siyen kuri'un ne.
"An fara bincike kuma za a mika sakamkon binciken ga hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC don daukar matakin da ya dace," ya ce.
Kamar yadda ya ce, an tura jami'an 'yan sanda 6,726 tare da wasu jami'an cibiyoyin tsaro wajen zabukan.
"An samar da taro isasshe a rumfunan zabe 864 da kuma dakin hada sakamakon zabukan a kananan hukumomin da abin ya shafa a jihar."
Kakakin rundunar 'yan sandan ya tabbatar da cewa zaben maye gurbin an shi ne cikin lumana da salama a yankin kuam babu wani mummunan lamarin da ya auku yayin zaben.
Ya jinjinawa jama'ar jihar ta yadda suka bada goyon baya da hadin kai yayin zaben maye gurbin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng