'Yan bindiga sun sace dalibin FGC mai shekaru 17 a Abuja

'Yan bindiga sun sace dalibin FGC mai shekaru 17 a Abuja

Da safiyar ranar Talata ne rahotanni suka bayyana cewa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka sace wani dalibi mai shekaru 17 dake karatu a makarantar sakandare ta tarayya (FGC), Rubuci, a birnin tarayya (FCT), Abuja.

An sace dalibin mai suna, Gift Abiikor, a gidan wani mutum mai suna Ahmed Adamu wanda gidansa ke daf da makarantar FGC Rubuchi.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe daya na dare yayin da Abiikor ya bi abokansa zuwa gidan mahaifinsu, Ahmed Adamu.

Da yake sanar da rundunar 'yan sanda a kan sace Abiiko, Adamu ya bayyana cewa 'yan bindigar sun shiga gidansa da tsakar dare yayin da Abiiko da 'ya'yansa ke bacci a dakinsu, inda suka tashi matashin suka tafi da shi.

'Yan bindiga sun sace dalibin FGC mai shekaru 17 a Abuja
'Yan bindiga
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa data fito daga hedikwatar rundunar 'yan sandan Abuja, kwamishinan 'yan sanda, CP Bala Ciroma, ya bayar da umarnin a fara gudanar da bincike a kan sace matashin.

Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin rundunar 'yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manzah, ta ce, "a cewar Ahmed Adamu, mutumin da ya kawo mana rahoto, wasu mutane dauke da bindigi sun shiga gidansa da misalin karfe 1000hr na dare tare da sace Gift Abiiko wanda ke kwance gado daya tare da 'ya'yansa.

DUBA WANNAN: Hukumar yaki da cin hanci ta Kano ta kama ma'ajin fadar sarki Sanusi II

"Wannan abu marar dadi ya faru ne a gidan Ahmed Adamu dake daura da harabar makarantar Sakandire ta gwamnatin tarayya dake Rubochi.

"Rundunar 'yan sanda tana mai bawa jama'a tabbacin cewa tana iyakar bakin kokarinta domin ceto matashin tare da gano duk wata sakarkakiya data kai ga yin garkuwa da shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel