Yanzun nan: An dakatar da wasu sarakuna 2 a Zamfara

Yanzun nan: An dakatar da wasu sarakuna 2 a Zamfara

- Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dakatar da wasu sarakunan gargajiya guda biyu

- Sanarwar ta fito ne daga ma’aikatar harkokin kananan hukumomi da masarautun jihar sannan kuma cewa tuni dakatarwar ta fara aiki tun daga ranar Litinin, 27 ga watan Janairu

- Mai ba gwamna shawara a kan masarautu, Alhaji Yusuf Abubakar Zulum, ya ce sun samu umurnin ne daga sakataren gwamnatin jihar cewa a dakatar dasu kan wasu laifuffuka da suka aikata

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dakatar da wasu sarakunan gargajiya guda biyu a jihar.

Sanarwar ta fito ne daga ma’aikatar harkokin kananan hukumomi da masarautun jihar, kuma sanarwar ta bayyana cewa tuni dakatarwar ta fara aiki tun daga jiya Litinin, 27 ga watan Janairu.

Dakatarwar ta shafi Alhaji Bello Garba Kanwa, sarkin yakin zurmi daga masarautar Zurmi, babba uban kasar kanwa da Alhaji Muhammad Bello Yusuf na III, Marafan Bakura, babba uban kasar Bakura.

Yanzun nan: An dakatar da wasu sarakuna 2 a Zamfara
Yanzun nan: An dakatar da wasu sarakuna 2 a Zamfara
Asali: Facebook

A wata hira tare da shafin BBC Hausa, mai ba gwamna shawara a kan masarautu, Alhaji Yusuf Abubakar Zulum, ya ce sun samu umurnin ne daga sakataren gwamnatin jihar cewa a dakatar dasu kan wasu laifuffuka da suka aikata. Ya kuma bayyana cewa za su fitar da jawabi kan laifuffukan da suka aikata nan gaba kadan.

Ya kuma bayyana cewa dakatarwar nasu zai ci gaba har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buratai ya sake bude hanyar Maiduguri-Damboa bayan watanni 13 a rufe

Sai dai wasu na zargin cewa akatarwar nasu na da nasaba belin wasu yan jam’iyyar APC da suka karba bayan an kama su tare da gurfanar dasu a gaban kotu.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya yabawa matakin da gwamna Bello Matawalle ya dauka wajen dakile yan bindiga, masu garkuwa da mutane da yan barandan a jihar Zamfara.

Shugaban kasan ya bayyana yabonsa ne a jawabinsa na taron yaye daliban jami'an tarayya dake Gusau, babbar birnin jihar Zamfara.

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa rikicin da ya kwashe kimanin shekaru goma a jihar ya fara sauki bisa ga shirin sulhu da gwamnan ya samar.

Buhari ya ce wannan shiri ta haifar da 'da mai dio wajen ceto wadanda akayi garkuwa da su tare da amsan makaman yan bindiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel