Motocin APC zan fara kamawa kan harajin hotunan jam’iyya – Shugaban Karota

Motocin APC zan fara kamawa kan harajin hotunan jam’iyya – Shugaban Karota

- Shugaban hukumar da ke kula da ababen hawa na jam’iyyar jahar Kano, Dakta Baffa Babba Dan Agundi, ya bayyana cewa zai yi aiki na ba sani ba sabo a kan dokar biyan haraji kan hotunan siyasa kan ababen hawa

- Dan Agundi ya ce tuni ya biya wa motocinsa guda biyu masu dauke da hotunan Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma hoton jam’iyyarsa ta APC kudin haraji a matsayinsa na mai bi da mutu ta doka

- Ya ce idan har motocin jam’iyyarsa ta APC suka ki biyan harajin, toh shakka babu ta kan motarsu zai fara aiwatar da dokar ta hanyar kama su

Rahotanni sun kawo cewa Shugaban hukumar da ke kula da ababen hawa na jam’iyyar jahar Kano, Dakta Baffa Babba Dan Agundi, ya bayyana cewa ya jima da biya wa motocinsa guda biyu masu dauke da hotunan Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma hoton jam’iyyarsa ta APC kudin haraji a matsayinsa na mai bi da mutu ta doka.

Ya ce ya yi hakan ne daidai da yadda dokar biyan haraji ta tanada, cewa sanya hotunan wani dan siyasa a ko wani hoto da doka ya yarda dashi a ababen hawa wajibi ne a biya haraji.

Saboda haka Dan Agundi ya ce dole kowa ya bi doka ta hanyar biyan harajin kamar yadda shima ya yi.

Motocin APC zan fara kamawa kan harajin hotunan jam’iyya – Shugaban Karota
Shugaban Karota ya ce motocin APC zai fara kamawa kan harajin hotunan jam’iyya
Asali: Twitter

Shugaban Karotan ya yi wannan jawabi ne a yayinda Shugaban jam’iyyar APC na mazabar Fagge, Alhaji Nafi’u Shehu ya kai masa ziyara ofishinsa tare da magoya bayan jam’iyyar.

Ya kuma umurci jam’iyyarsa da sauran jama’a da su bi doka ta biyan harajin sanya hotuna a ababen hawa domin doka za ta fara aiki kan duk wanda bai biya ba, kuma sannan cewa dokar za ta kasance ta ba sani ba sabo.

KU KARANTA KUMA: KAROTA zata fara kwacen adaidaita marasa rijista a Kano

Daga karshe ya ce idan har motocin jam’iyyarsa ta APC suka ki biyan harajin, toh shakka babu ta kan motarsu zai fara aiwatar da dokar ta hanyar kama su. Don a cewarsa an kafa gwamnatin APC ne don tabbatar da doka kan kowa ba tare da wariya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng